Connect with us

Fasaha

Hanyoyin gane bidiyon boge da akayi amfani da fasaha wajan sauya abubuwa

Published

on

Yadda ake gane bidiyon bagi

Bidiyon da yake wannan likau din na daya daga cikin dubban bidiyon boge na “deepfake” da suke yawo a shafukan sada zumunta. A hakika abin da ya faru a bidiyon bai faru a gaske ba. Kirkirarsa akai amma aka yi shi mai kama gaske.

Fasahar “deepfake” na kirkirar bidiyon da yake kamar gaske duk ko da kuwa kirkirarre ne. Ta hanyar ake kirkirar bidiyon da yake kama da mutum na aikata abin da bai taba aikatawa a rayuwarsa ba.

Masu bincike a jami’o’i ne suka fara gano yadda za su iya amfani da kwamfuta wajen kirkirar bidiyon a wajejen 1990. Daga baya masu fina-finai suka karbi lamarin.

A yanzu kuwa fasahar ta fada hannun matasa ‘yan dandatsa da suke amfani da ita wajen kirkirar bidiyoyin da suke sakawa a shafukan sada-zumunta ko kuma bidiyoyin batsa.

Ba iya bidiyo ba, har sauti ana iya kirkirarsa ta hanyar “deepfake”. Akwai “applications” na waya masu yawa da ake amfani da su wajen kirkirar muryar wani ta hanyar fasahar daga cikinsu akwai “VoiceApp” da “Overdub”.

Wannan fasahar ta samar da damar kirkirar bidiyon boge da kuma muryar boge. Ana iya kirkirar muryoyin sanannun mutane ta hanyar suna fadar maganganu da ba su fada ba a zahiri.

Hanyar Damfara

Jaridu sun rawaito yadda aka yi amfani da bidiyon bogi wajen damfarar mutane ta hanyar yanar gizo ciki kuwa har da wanda aka yi amfani da bayanan wani kamfani a Birtaniya wajen damfarar da ta kai kimanin £200,000.

A wani rahoto da jaridar Forbes ta rubuta, wani dan damfara ya yi amfani da muryar bogi wajen kwaikwayar muryar shugaban kamfanin har ya ce a fitar da wadannan makudan kudade.

Rahoton ya bayyana yadda dan damfarar ya kira sashin kudi na kamfanin ya ce a fitar da wannan kudi, sannan ya sake kira ya ce ya tabbatar da shigar kudin.

A lokacin da dan damfarar ya kara kira don a tura kudi a karo na biyu sai mai tura kudin ya lura cewa lambar mai kiran ta kasar Australia ce ba ta Birtaniya ba.

Yaduwa Kamar Wutar Daji

Rahotanni sun nuna cewa bidiyo da muryoyin bogi na “deepfake” na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

Rahoton wani kamfani da yake bibiyar fasahar kirkirar da ake kira Deeptrace ya nuna cewa a shekarar 2019 akwai bidiyon bogi a intanet da suka kai yawan 7,965.

Rahoton ya ce a kasa da wata tara yawan bidiyon ya karu zuwa zuwa 14,678, wanda hakan ke nuna bidiyon “deepfake” ya karu zuwa ninki biyun yawansa tun farkon kirkirar fasahar a kasa da wata tara kawai.

A yanzu haka idan ka yi binciken “deepfake” a shafin bincike na Google zai samar maka da dubunnan bidiyoyin bogi musamman a shafin YouTube da kuma sauran shafukan bidiyon batsa.

Aliyu Dahiru Aliyu matashi ne mai bincike kan abin da ya shafi labaran karya, mai sharhi ne kuma marubuci kan al'amuran yau da kullum a shafukan sada zumunta
Bayanan hoto, Aliyu Dahiru Aliyu matashi ne mai bincike kan abin da ya shafi labaran karya, mai sharhi ne kuma marubuci kan al’amuran yau da kullum a shafukan sada zumunta

Siyasar Zamba

Ana ci gaba da amfani da bidiyoyin bogi wajen kirkirar bayanan da ake zambatar mutane da su a siyasa.

Masana na ganin yawaitar irin wadannan bidiyoyi ka iya janyo tashin husumar siyasa, rigingimun addini, da kuma lalata dimokradiyya da ci gaba.

Masanan na ganin yawaitar irin wadannan bidiyoyi zai janyo mutane su daina yarda ko su dinga shakkun bidiyon da a hakika na gaskiya ne.

Wani masani a bangaren bidiyon bogi dan kasar Birtaniya da ake kira da John Dabson, ya bayyana cewa yawaitar irin wadannan bidiyoyi zai iya rusa yardar da aka yiwa dimokradiyya.

A shekarar 2018, wani bidiyo da mutanen Gabon suka dauka kirkirarsa aka yi don a boye rashin lafiyar Shugaba Ali Bango ya janyo tashin hankalin siyasa a kasar.

Yadda Ake Gano Bidiyon Boge

Deepfake

Har yanzu haka fasahar gane bidiyon boge ba ta gama yin nisa ba saboda shi kansa bidiyon a yanzu yake yaduwa.

Wasu fasahohin da aka ce suna iya gane bidiyon boge ta hanyar motsin fuskar mutum basu yi ingancin da ake da bukatarsu ba.

Sai dai kamfanin Facebook na ci gaba da samar da hanyoyin da za a hadu wajen samar da maganin wannan matsala tun ba ta yi nisa ba a wani taro da ake kira da “Facebook Deepfake Detection Challenge”.

Da farko bincike a kamfanin Deeptrace sun gano cewa mutanen da suke bidiyon boge na “deepfake” ba sa motsa idanuwansu. Amma a watanni kadan masu kirkirar suka fara yin bidiyon mai motsa idanun.

Har yanzu dai bidiyon boge bai kai kyau da fitar bidiyon gaske ba. Amma masana na ganin yarda cewar bidiyoyin ba za su taba kamo na gasken ba yaudarar kai ne.

Babbar hanyar da aka umarci mutane su dinga amfani da ita wajen gane bidiyon boge shi ne amfanin da zurfin tunani wajen gane shin lamarin zai yiwu ko ba zai yiwu ba.

Tushen Labarin

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku