Connect with us

Kwamfuta

Hanyoyin Inganta saurin Kwamfuta da Wayoyin Hannu

Published

on

inganta saurin kwamfuta da wayar hannu

Hanyoyin Inganta Saurin Kwamfuta da Wayoyin Hannu.

Wannan batu ya taso ne abisa korafe-korafen Jama’a masu ta’ammali da Na’urorin Kwamfuta da Manyan Wayoyin Hannu da kullum ake amfani da su domin gudanar da al’amuran yau da kullum.

Ta’ammali da Kwamfuta ko Wayar hannu ya zamo jigo a rayuwar jama’a domin gudanar da aiyukan yau da kullum, kama daga; Kasuwanci, Fannin Ilimi, Fannin Lafiya, Bincike, Fannin Tsaro, Aiyukan Kotu, Nema da yada labarai da sauran al’amura masu yawan gaske.

Ilimin sarrafa kwamfuta da Wayar Hannu ya zama mai saukin gaske. Duba da yadda ake ta kara inganta su da kuma saukaka fahimtar yadda za’a sarrafa su ko da mutum ba shida ilimin zamani a halin yanzu za muga kusan kowa yana da wayar hannu ko kwamfuta koma dukkan su, babu babba babu yaro.

Yawaitar amafani da na’urori domin bukatun yau da kullum, yanada alaaka da saukin mallakarsu, koda yake masu iya magana sunce iya kudin ka iya shagalin ka. Dukkanin wadannan na’urori sunyi tarayya wajan abubuwa kamar haka; Saurin Sarrafa aiki, Rumbun adana abubuwa ko kayan da aka sarrafa, Ababen dogaro yayin gudanar da aiki, saukin dauka ko rikewa a hannu yayin zurga-zurga da saun su…

Rashin samun abubuwa 2 zuwa 3 daga cikin wadancan siffofi da na bayyana, yakan haifar da damuwa wajan sarrafa na’ura. Kwamfuta da wayar hannu sukanyi nauyi ko jinkiri wajan sarrafa aiyuka, saboda dalilai masu yawa. Amma zanyi bayani akan wadanda suka fi muhimmanci.

  1. Cutar Na’ura mai yaduwa (Virus): Sanin kowane cutar na’ura ta virus da dange-dangen ta suna taka rawa wajan sauya akalar sarrafa na’ura, sukan cutar da ita suna hana ta yin aiki kamar yadda aka tsara ta, taki gaba taki baya. Amfani da manhajar magance (anti-virus) su yanada matukar muhimmanci.
  2. Cinkushe na’ura da manhajoji ba bisa ka’ida ba: Wasu mutane suna da akidar saka manhajoji iri-iri masu yawa koda basu iya aiki da su ba. Yin hakan yana haddasa cinkushewar rumbun adana aiki (memory). Saboda cire manhajar da ba’a amfani da ita yana bunkasa aikin na’ura cikin sauri.
  3. Sarrafa na’ura a cikin yanayi mai zafi: Sarrafa na’ura a cikin yanayin zafi, ko waje maras isashshiyar iska yana haddasawa sassan ita na’urar jinkirin aiki. Wanda hakan yana jawo koma baya ga ingancin na’ura. Dan haka idan babu na’urar sanyaya daki sai a kunna fanka, idan iatama babu to sai a bude kofofi da winduna domin iska ta dinga ratsa su a lokacin da ake aiki.
  4. Rashin sabunta manhajoji akan lokaci: Haka wannan ma babban al’amari ne da yake jawo tarnaki ga na’ura. Sabunta manhaja (update) akan lokaci yanada amfani domin yana magance duk wata matsala tattare da ita kanta manhajar da sauran sassan na’ura dake aiki da manhaja yayin gudanar da aiki.
  5. Amfani da gurbatattun Manhajoji: Gurbatattun manhajoji na da illa ga na’ura. Domin sukan zamo ummul’aba’isin bude dukkan kofofin sirri na na’ura domin cututtuka masu yawa su shiga. Kuma sukan zamo makamai da masu kutse ke amfani da su wajan cutar da al’umma. Kuma anfi samun su a manhajoji na kyauta (free). Amfani da sahihan manhajoji shi ne mafi dacewa ga jama’a.
  6. Datti ko kura a cikin na’ura: Rashin tsaftace na’ura ko dakunan da ake amfani da ita, harma da teburin da aka dorata idan ta girke ce (desktop), yanada matukar illa, wajan toshe kofofin shakar iska ga ita na’urar, har ma lalacewar wasu sassa saboda tsabar datti da kura. Dan haka kulawa da tsaftar na’ura yana inganta sassan ta yadda zatayi aiki cikin nishadi.
  7. Katsewar wutar lantarki yayin da ake tsaka da aiki: Daukewar wutar lantarki a lokacin da ake tsaka da gudanar da aiki da na’uara, ko karewa batir saboda rashin caji, babbar matsalace. Hakan yana haddasa matsala ga rumbun adana aiki (Hard Disk Drive) kuma yana haddasa jinkiri wajan gudanar da aiyuka. Amfani da na’urar adana wutar lantar ki (UPS) da kuma isashshen caji ga wayoyi ko kwamfuta laptop, zai taimaka kwarai, ko kuma idan an dauke wuta sai a kashe a hakura har sai an sami wuta ko inji.
  8. Da sauran su…

Kadan kenan daga cikin dalilan da suke haddasa nauyi ko jinkiri wajan gudanar da aiki ga na’ura, wadanda idan aka magance su kamar yadda aka tsara to za aji dadin sarrafa na’ura ba tare da samun jinkiri ko nauyi ba a yayin gudanar da aiki. Bugu da kari, daga darajar rumbun aiki (RAM Upgrade), yana bunkasa na’ura ta fuskar sauri wajan gudanar da aiki.

Dafatan Allah ya amfanar damu baki daya.