Connect with us

Featured

Hanyoyin Rage Zukewar Cajin Waya

Published

on

Hanyoyin Rage Zukewar Cajin Waya

Hanyoyin Rage Saurin Zukewar Cajin Waya

Kasancewar wayoyin zamani da ake amfani dasu a wannan lokaci suna da tsare-tsare daidai da zamani, kuma ana gudanar da aikace-aikacen yau da kullum da su, kamar yadda ake sarrafa Kwamfuta wajan gudanar da aiyuka masu yawan gaske. Sannan kuma ana fama da saurin zukewar caji a lokutan da ake tsaka da amfani da su.

SCREEN BRIGHTNESS

Hasken screen, wannan ma hanya ce dake jawo saurin zukewar caji a Wayoyi. Hakan ya sa zaku ga akwai tsarin sarrafa haske a kowacce Na’ura, akwai wanda yake Auto; dakanta wayar zata sarrafa hasken a wurare daban daban. Idan mutum yana waje mai duhu zata kara hasken screen daidai misali, haka idan yana cikin haske zata kara shi yadda zai iya gani da sarrafa wayarsa. Sannan akwai tsarin wanda mutum zai iya karawa da kansa daga 1 – 100 wato manual kenan. Saboda haka rage haske a screen na waya zai taimaka wajan rage shan caji. Bayan saurin zukewar caji da hasken screen ke haddasawa, akwai matsala da yake ahifarwa ga lafiyar idon bil’adama.

SOUNDS

Wato sautin Karar shigowar Kira a Waya ko alarm da sauran su. Zaku ga akwai wadanda ake yawan kiran su ko aiko musu da sakonni akai-akai, kuma sun bar karar wayar su a mataki mai kara sosai wanda hakan yana sa cajin waya ya zuke da wuri. Saboda haka zai fi kyau a rage Volume daidai misali hakan zai rage shan caji a waya. Sai dai akwai yanayin wajan da mutumu yake gudanar da harkokin sa kamar kasuwa ko inda yake da hayaniya sosai. Wannan dalili ne da zai sa mutum ya kure sautin karar wayar sa, daga baya kuma sai ya rage idan ya bar wajan.

WALLPAPER

Musamman masu launika, masu ado  ko Masu mosti. Suna bada gudummawa wajan shanye cajin waya. Saboda zaku ga suna da haske sosai, hakan ya sa suke saurin zuke cajin waya da wuri. Saboda zaifi kayu ace mutum ya yi amfani da wallpaper wadda bata da launika masu yawa kuma ba mai haske sosai ba.

SCREEN ROTATE

Wato juyawar screen a waya; tsaye ko a kwance. Barin sa a kunna yana sa zukewar caji a waya da sauri. Saboda Sensor din wayar nake yake lura da yadda aka rike waya, sannan ya juya screen

BACKGROUND APPLICATIONS

Akwai mutane masu bude abubuwa da yawa a wayoyin su. Idan suka shiga wani application zasu yi minimaizin, sai su shiga wani, shima suyi minimaizin su sake shiga wani, haka dai suke yi kullum. Ba tare da sunyi tunanin cewa dukkanin applications din da aka bude suna ci gaba da aiki a boye. Kuma daga cikn su akwai apps dinda suke amfani da Ram, Storage, Camara, wasu da Map da sauran su. A taikace an cikata dai aiyuka masu yawa a lokaci guda. Wannan itama babbar hanya ce dake zuke cajin waya. Saboda zaifi kyau a duk lokacin da aka gama amfani da application a kasha shi gaba dayakafin a bude wani. Hakan zai karawa Waya saurin sarrafa aiki kuma bazata zuke caji da wuri ba.

BATTERY SETTING

Duba bangaren setting na battery yanada matukar muhimmanci domin ganin applications masu zukar caji da yawa ko applications marasa amfani a lokacin. A battery setting ne ake iya sarrafa yadda applications za su yi amfani da battery. Hakan zai taimaka kwarai wajan rage saurin zukewar caji a waya.

NOTIFICATIONS

Shima wannan hanyace wadda ke sa zukewar caji da wuri. Saboda a duk lokacin da sako ya fado cikin waya sai ta yi Haske, Kara har da Vibration. Kuma zaku ga akwai wanda yake amafni da manhajar whatsapp kuma yan cikin group babu iyaka, a duk lokacin da aka yi sharing daga wadannan group sai wayarsa tayi Notifying dinsa akan shigowar sakonnin komai yawan su. A kowanne lokaci sako ya shigo waya sai tayi haske ko kara kuma idan kun duba akwai applications masu yawa da suke amfani da notification, Text Messaging, WhatsApp, Twitter, Facebook, Instagram da sauran su… Saboda haka idan akwai application din da bakwa bukatar notification dinsa sai ku shiga setting na application din zaku ga inda akace Notification Setting daga nan sai ku kashe shi, yin hakan zai rage shan caji a wayoyin ku.

VIBRATION

Shima hanya ce dake sa saurin shan caji a waya. Akwai wadanda kullum wayar su a vibration take amma akwai dalilin yin haka. A duk lokacin da kira ya shigo ko notification wayar za ta girgiza domin ankarar da mai ita. Hakan yana haddasa saurin karewar caji. Dan haka zaifi kyau mutum ya lura da lokacin da ake da bukatar amfani da vibration da kuma lokacin da ba a bukatar sa. Ta haka ne za a rage saurin zukewar caji a waya.

WIFI, BLUETOOTH DA MAP

Barin wifi, Bluetooth da Map a bude bayan an kamala amfani da su kamar sharing ko bincike. Hakan yana saurin karewar caji a waya. Saboda barin su a bude sune cikin aikine na bincike ko da anyi minimizing din su. Zaifi kyau a kasha su a duk lokacin da aka gama amfani da su.

TEMPERATURE

A lokacin zafi wayoyi sun fi samun matsalar karewar caji da sauri.  Haka zalika idan aka saka caji shima baya saurin a lokaci ko yanayin zafi. Saboda haka zai fi kyau a sarrafa waya a wajan da babu zafi sosai.

A takaice wadannan sune abubuwan da suke haddasa saurin zukewar caji a karshe ma suka she battery ba tare da mutane sun sani ba. Dan Haka sharace na ke bayar wa akan lura da dukkan abubuwanda na bayyana a sama, saboda a sami saukin matsalar caji.