Connect with us

Kimiyya

Hotunan Ban Mamaki Daga Duniyar Mars

Published

on

hotuna daga duniyar mars

Mutum-mutumin Perseverance na hukumar sararin samaniyar Amurka Nasa ya sauka a Duniyar Mars ranar 18 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:55 na dare agogon GMT, bayan tafiyar wata bakwai da ya shafe yanayi daga duniyar Earth.

Tun daga sannan, ya yi ta aiko hotuna masu kayatarwa daga inda ya sauka a duniyar, wato yankin Ramin Jezero, mai fadin kilomita 49 da zurfin mil 30 daga arewacin tsakiyar Jar Duniyar.

Ga dai wasu zababbun hotuna da mutum-mutumin ke aikowa, a yayin da yake ci gaba da neman wata alama ta ko an taba yin rayuwa a can, da kuma gano yadda yanayin kasa na duniyar yake da yadda sauyin yanayinta yake da kuma kwaso kasar wajen.

First image taken from the High Resolution Imaging Experiment camera aboard Nasa's Perseverance Rover on the surface of Mars (19 February 2021)

Bayanin hoto: Hoton farko na mutum-mutumin Perseverance da aka dauka da kyamara mai fito da hoto fes-fes da ke jikin Perseverance. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/MSSS

1px transparent line
Colour image of Mars taken by the Hazard Cameras on the underside of Nasa's Perseverance Mars rover

Bayanin hoto: Wannan shi ne hoto na farko wanda ya fito fes mai kala da kyamarorin suka aiko bayan saukar mutum-mutumin. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech

1px transparent line
Enhanced colour image of the rover taken by the Mars Reconnaissance Orbiter high above the planet

Bayanin hoto: Ana iya hango Perseverance a wannan hoton mai kala a daidai inda ya sauka, kwana shida bayan saukarsa. Za ku iya ganin wasu bangarori biyu masu haske daga gefen mutum-mutumi. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/UArizona

Perseverance yana dauke da wasu manyan na'urori na kimiyya da zu su tattaro bayanai a kan yanayin kasar duniyar, yanayin samaniyarta da kuma yanayin, muhallinta. Kyamarar da ta dauki wannan tana makale ne a kan turken da ke jikin mutum-mutumin.

Bayanin hoto: Perseverance yana dauke da wasu manyan na’urori na kimiyya da zu su tattaro bayanai a kan yanayin kasar duniyar, yanayin samaniyarta da kuma yanayin, muhallinta. Kyamarar da ta dauki wannan tana makale ne a kan turken da ke jikin mutum-mutumin. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech

1px transparent line
Nasa's Perseverance Mars rover deck (20 February 2021)

Bayanin hoto: Nan hoton wani sashe na jikin na’urar ne da zai dinga gano alamomin sinadarai. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech1px transparent line

Mars surface captured by onboard Right Navigation Camera (Navcam), 1 March 2021

Bayanin hoto: Akwai kuma wata kyamara da ke daukar hotuna na kurkusa na duwatsu da kasar wajen. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech

1px transparent line
A panorama, taken on 21 February, by Mastcam-Z

Bayanin hoto: Wannan ne hoto na farko da kyamarar ta dauka a zagaye. An dauka da kyamarar Mastcam-Z, da kuma wata da ke jikin na’urar. An hade bidiyon ne daga duniyar Earth daga hotuna 142 daban-daban. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSSS

 
This wind-carved rock seen in first 360-degree panorama taken by the Mastcam-Z instrument

Bayanin hoto: Wannan dutsen an sa masa suna “harbour seal”, saboda wasu dalilai. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSS

A detail shot from the top of the panorama shows the rim of Jezero Crater

Bayanin hoto: Wannan hoton na nuna yawan bayanan da ake samu daga abin da kyamarorin ke dauka. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU/MSSS

Mars surface using Left Mastcam-Z camera

Bayanin hoto: Shi kuma wannan hoton an dauke shi ne da idon hagu na kyamarar Mastcam-Z. Kyamarorin hagu da na daman suna kusa da juna kuma suna kallon waje daya, inda suke dauko yanayin da ko a zahiri haka za a gani. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU

1px transparent line

Mars surface using Left Mastcam-Z camera

Bayanin hoto: Bayan kwanaki biyu, sai aka dauki wannan hoton da waccar kyamarar dai, kuma wannan hoton shi aka zaba a matsayin “hoton mako” a cikin mako na biyu na saukar Perseverance a Mars. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech/ASU

Section of layering in a delta on the surface of Mars

Bayanin hoto: Wannan hoton kuma idon dama na kyamarar Mastcam-Z ne ya dauke shi, wani tsohon yanki ne na waje mai damshi a Jezero, wanda ya ware daga ainihin yankin sakamakon zaizayar kasa tsawon lokaci. Kasar da ke nan wajen na daya daga cikin manyan ayyukan kimiyya da ake son mutum-mutumin ya yi don gano rayuwar farko da aka yi a wajen. – Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech/ASU

1px transparent line
Mars Perseverance Descent Stage Down-Look Camera image

Bayanin hoto: Hotunan farko da suka fara isowa duniyar Earth na saukar na’urar ce a duniyar Mars. – Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech

Parachute shot from the spacecraft's backshell during descent

Bayanin hoto: Wannan hoton ma an dauke shi a lokacin saukar. Inda ya rage kilomita 11 na’urar ta dira kasa, a lokacin da lemar taimaka wa wajen saukata ta bude. – Asalin hoton, Nasa/JPL-Caltech

The surface of Mars directly below Nasa's Mars Perseverance rover is seen using the Rover Down-Look Camera (22 February 2021).

Bayanin hoto: Wannan hoton na nuna dandaryar kasar duniyar Mars ne da ke kasan na’urar. – Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech

The surface of Mars directly below Nasa's Mars Perseverance rover is seen using the Rover Down-Look Camera

Bayanin hoto: Ga wani hoton ma da aka dauka yana kallon ramin Jezero a yayin da na’urar ke sauka. – Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech

An zuba tallafin kudi da zai sa Na’urar Perseverance ta shafe shekara daya a duniyar Mars tana aiki, wanda ya yi daidai da shekara biyu a duniyar Earth.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku