Connect with us

Fasaha

Illolin dake tattare da Fasahar zamani

Published

on

illolin da ke tattare da fasahar zamani

Illolin dake tattare da Fasahar zamani. Wannan shi ne batun da nakeso na yi bayani akai, kasancewar duk abubuwan da muke tattaunawa a baya muna magana ne akan cigaban da Fasahar Zamani ta haifar a duniya.

Fasahar Zamani, tana cinkushe da tarin matsaloli ko ince illoli, kamar yadda amfanin ta yake a fadin duniya ta fuskar kere-kere da samun saukin aiwatar da dukkan aiyukan mu na yau da kullum cikin hanzari. Kusan illolin ta sunfi amfanin ta a duniya. Zanyi magana akan wasu muhimmai daga cikin su. Kuma akwai bukatar kowa ya san su, domin daukar matakin kare kai a kowanne lokaci.

 1. Bata lokaci mai muhimmanci; hakika mutane suna amfani da na’urorin fasahar zamani wajan gudanar da wasu al’amura da basu da ma’ana a rayuwar su, wanda hakan yana taka muhimmiyar rawa wajan bata lokutan su. Kuma lokaci tsada gare shi. Suna bata lokaci wajan Kallo talabijin, wasanni ta na’ura (games), sauraron kide-kide, wayoyin zamani da sauran su… Kuma sukanyi amfani da wadancan na’urpri ne musamman a lokutan aiki, karatu kai harma zuwa lokacin bacci wanda yin hakan kan ci lokaci ba tare da sun san hakan ba.
 2. Toshe kwakwalwa; tabbas wannan ma babbar illace, musamman yadda wasu suka ta’allaka dukkan tunanin su wajan amfani da na’ura a kowanne lokaci babu kakkautawa. Ba saiya amfani da tunanin su ko kwakwalwar su wajan yin aiki kamar; yin nazari, lissafi, warware matsala, fikira ko hazaka da sauran su… A kowanne lokaci sai sunyi amfani da na’ura wajan warware matsala komai kankantar ta.
 3. Kebanta daga cikin jama’a; ko ince rashin zama cikin jama’a. A lokuta da dama saboda dabi’antuwa da na’urorin zamani da jama’a kanyi, sukan kebe kan su daga cikin mutane, kullum suna cikin sarrafa na’ura musamman wayoyin zamani da wasannin games, tauraron dan adam (Satellite) da sauran su…
 4. Gurbata Mahalli; a lokuta da dama akan sami matsalolin gurbatar yanayi saboda fasahar zamani, musamman a unguwannin dake kusa da masana’antu. Manyan ijina ko ince na’urorin zamani da ake amfani da su wajan sarrafa abubuwa ko kerekere kan fitar da munanan abubuwan dakan gurbata muhalli ta fuskoki da yawa kamar haka; Gurbatar isakar da muke shaka yadda zata kai ga yiwa al’umma illa ga rayuwar su. Akwai dattin kanfanoni dake gurbata ruwan sha, wanda shi ma ahakan babbar illa ce ga rayuwar dan adam. Sannan kuma akwai na’urori masu kara a lokacin da ake sarrafa su, wadda wannan kara da sukeyi itama kan iya zama barazana ga lafiyar al’umma ta wajan illata sassan jikin dan adam da suke da ruwa da tsaki wajan sauraro kamar dodon kunne har ma da kwakwalwa.
 5. Damfaruwa (addiction) da Fasahara zamani; wannan ma babbar matsala ce da tafi karfi ga matasa, ta yadda a kowanne lokaci basu da wani aiki sai sarrafawa ko mu’amala da na’urorin fasaha. A ko ina suka tsinci kansu basu da wani aiki sai sarrafa na’ura. Har su kan manta da cin abinci ko wasu muhimman abubuwa na rayuwar su a lokacin da suke sarrafa na’urorin fasaha. A takaice basa iyayin komai a rayuwar su.
 6. Kore sha’awar karatu ko nazari; musamman ga matasa. Akwai matasan da yawan amfani da na’urori fasahar zamani kan hana su yin nazari ko bincike a fannini neman ilimi, koma ya cire musu sha’awar yin karatun gaba daya. hakan shi ma babbar illa ce ga rayuwar matasa a fadin duniyar nan.
 7. Rashin aikin yi; a wasu lokuta aakan rage ko sallami ma’aikata masu yawan gaske daga ma’aikatu saboda amfani da na’urorin fasahar zamani wajan gudanar da dukkan aiyuka. Wadanda basu da ilimin sarrafa na’urorin fasahar zamani kan rasa aiyukan yi a fadin duniya baki daya.
 8. Damfarar Al’umma; ana amfani da fasahar zamani wajan damfarar al’umma ta hanyoyi masu yawan gaske. Musamman a wannan lokaci da al’amura suka ta’azzara. A kullum mukan ji a kafar sadarwa ta Radio cewa anyi kutse a shafukan intanet ko an zambaci jama’a ta hanyoyi masu yawa an kwashi bayanan sirri ko makudan kudade a bisa dalilin amfani da fasahar zamani. Misali akwai kungiyoyin matasa masu fahimta akan yadda al’amuran fasahar zamani ke wakana irn su yahoo boys da sauran su…
 9. Barnatar da Kudi; a wasu lokutan mutane sukan kashe makudan kudade wajan mallakar na’urori domin gudanar da aiyukan yau da kullum. Haka zalika suna kashe kudade masu yawa wajan kula da na’urorin domin su kasance lafiya a kowanne lokaci. Dazarar an sake kera wasu na’urorin da suka fi wadanda suke amfani da su, nan take zasu sake kashe makudan kudade domin mallakar su. hakan yana faruwa a bisa danfaruwa da sukayi da na’urorin fasaha da kuma son a ce kullum sune kan gaba wajan fara siyan sababbin na’urorin zamani a nahiyar su.
 10. Illata lafiyar ‘Yan Adam; Fasahar zamani tana tattare da illoli ga lafiyar ‘yan adam musamman wadanda suka fi amfani da na’urori a rayuwar su ta yau da kullum. Ta kan haifar da matsaloli kamar haka; Kashewa ko lalata ido, Kashewa ko rage karfin jin sauti ga kunne, Sanya mummunar Kiba, Sankarar Kwakwalwa, haddasa larurar asma (asthma), cututtukan fata da sauran su…
 11. Yawaitar makamai a duniya; fasahar zamani tana taka babbar rawa wajan kirkirar mugayen makamai a duniya domin cimma manufar yaki da karin karfn tattalin arzikin wasu manyan kasashen duniya. Akwai makaman da basu dace ayi amfani da su a duniya ba. Bugu da kari, akan kirkiri cututtuka a matsayin makaman yaki a fadin duniya duk ta hanyar amfani da fasahar zamani.
 12. Tururi na’ura da na sadarwa; a lokuta da dama na’urori kan haifar da samuwar tururi a yayin da ake sarrafa su ko ake tsaka da aiki da su. Tururin ya kasu zuwa matakai daban-daban. Akwai masu illa nan take da kuma masu daukar lokaci suna ratsa jikin dan adam, wanda dukkansu babbar illa ce ga jiki da rayuwar dan adam. Shi yasa yawan ta’ammali da na’urori da ya wuce kima ko sadarwa mai karfin gaske kan zamo illa ga jikin dan adam.

Akwai illoli masu yawan gaske da fasahar zamani ce sanidiyar bullar su a fadin duniya, wanda na barwa masu karatu domin su bincika sugani da kan su.Da fatan Allah ya amfanar da mu, ya kuma kare mu daga dukkan sharri.

 

Continue Reading