Connect with us

Featured

Instagram zai danne shafin Twitter

Published

on

instagram zai shallake shafin twitter

Wani bincike ya gano cewa shafin sada zumunta na Instagram da aka fi amfani da shi wajen wallafa hotuna yana dab da wuce shafin Twtter a matsayin wani waje na samun labarai.

Binciken na kamfanin dillancin labarai na bangaren Reuters Institute Digital News na 2020 ya gano cewa amfani da Instagram domin yada labarai ya ninka sau biyu tun daga 2018.

Yadda matasa ke yayinsa ya nuna samun daukakarsa. Wanda hakan ke cewa kusan kashi daya cikin hudu na ‘yan shekara 18 zuwa 24 na amfani da Instagaram a matsayin wajen samun labaran da suka shafi korona.

Sai dai kafafen sada zumunta na cikin wuraren da ake samun labarai marasa tushe.

Kaso 26 ne cikin 100 kawai suka ce sun amince da kafafen sada zumunta wajen samun labaran da suka shafi Covid-19.

Irin wannan kason sun ce sun amince da mahajojin hira da abokai wajen samun labarai kamar su Facebook Messenger da WhasApp.

Amma gwamnati ta ce kafafen yada labarai sun samu amincewar mutane da kimanin kaso 59 cikin 100 idan aka kwatanta da na sada zumunta.

Amma Instagram yanzu na samun kusan kashi uku na wadanda suka amsa bayanai lokacin wannan binciken, kuma da kashi biyu cikin uku na ‘yan kasa da shekara 25.

Kuma kashi 11 cikin 100 cikinsu na amfani da shi ne wajen samun labarai, wanda yanzu ya zarce Tiwita da digo daya.

TUSHEN LABARI