Connect with us

Featured

Jack Dorsey ya ajiye mukaminsa na babban jami’in Twitter

Published

on

Jack Dorsey ya ajiye mukaminsa na babban jami'in Twitter
Jack Dorsey ya ajiye mukaminsa na babban jami'in Twitter

Kamfanin na Twitter ya bayyana cewa babban jami’in fasaha Parag Agrawal shi ne zai maye gurbinsa.

Jack Dorsey, wanda ya na cikin wadanda suka kafa Kamfanin Twitter a shekara ta 2006, ya kasance babban jami’in gudanarwa na Twitter da kuma kamfanin hada hadar kudi na Square.

” lokaci ya yi da zan tafi” a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannunsa, yana mai cewa kamfanin “a shirye ya ke ya ci gaba.”

Mista Dorsey ya ce yana da kwarin gwiwa a kan wanda zai maye gurbinsa. “Ina matukar godiya ga fasaharsa da kuma kwazonsa . Lokaci ya yi da zai yi jagoranci,” in ji shi.

A shekarar 2011 Mista Agrawal ya soma aiki a Twitter , kuma shi ne shugaban fasahar kamfanin tun 2017.

Cigaban Labari…

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku