Connect with us

Featured

Jack Dorsey ya sami kansa cikin rikita-rikita a Najeriya

Published

on

jack vs nigeria

Jack Dorsey, ya saba da ce-ce-ku-ce, amma a Najeriya ya sami kansa cikin rikita-rikita tsakanin matasan ƙasar da ke amfani da shafin da kuma gwamnati.

An sha yin amfani da dandalin nasa wajan haɗa zanga-zangar EndSars a shekarar da ta gabata, wadda ta zama wata ƙungiya mai adawa da cin zalin da ‘yan sanda ke aikatawa daga baya kuma ta koma rikici tsakanin matasa da ‘yan siyasa.

Sai dai kuma yanzu haka gwamnati ta garƙame dandalin nasa bayan Twitter ya goge wani saƙon Shugaba Buhari.

Jack Dorsey na burge ‘yan Najeriya da dama. Ayyukansa na samar da filin faɗar ra’ayi da kasuwanci ya dace da muradun matasa da ke jin cewa ana muzguna musu.

Duk da toshewar da aka yi wa dandalin nasa, Mista Dorsey ya ci gaba da wallafa abubuwa game da Najeriya kuma hakan ya ja hankalin wasu da yawa.

Yayin da ake gudanar da bikin Ranar Dimokuraɗiyya sannan wasu suka fito zanga-zangar neman a buɗe Twitter, Jack ya wallafa tutar Najeriya da alamar musabaha da kuma maudu’in “#bitcoin”.

Kauce wa Twitter, 1

 

🇳🇬🤝#bitcoin

— jack (@jack) June 12, 2021

 

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

 

Washegari kuma, ya yaɗa wata maƙala da ke kiran gwamnatin Najeriya ta bi tsarin kuɗin intanet na Bitcoin sannan ya ce “‘yan Najeriya za su jagoranci harkar #bitcoin”.

Wasu masana sun ce wannan ya nuna cewa Jack ɗan kasuwa ne kawai wanda ke neman tallata hajarsa.

Baya ga mallakar Twitter da aka fi saninsa da yi, kazalika shi ne ya mallaki manhajar Square and Cash App, wani kamfanin biyan kuɗi da ke harka da kuɗaɗen intanet musamman Bitcoin.

Hana amfani da kuɗin intanet (Bitcoin)

Kasuwar kuɗin intaent ta Najeriya, ita ce mafi girma a Afirka.

Hauhawar farashin kayan abinci da kuma faɗuwar darajar naira sun sa mutane da yawa sun koma amfani da kuɗin intanet, waɗanda wasu ke gani a matsayin mafi tsaro.

“A ko da yaushe sai an samu wata hanya da za ta bai wa ‘yan Najeriya damar samun sauƙi da yin tattali a kuɗaɗen da ba naira ba,” a cewar Faith Babafemi, wata ƙwararriya kan kuɗin intanet.

Ta ce akwai yanayin da kamfanonin Mista Jack za su amfana idan har aka ci gaba da amfani da kuɗin intanet a Najeriya.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku