Connect with us

Featured

Jack Dorsey ya yi bayani akan rufewar Twitter

Published

on

Shafin Twitter

Twitter ya dawo a daren Alhamis bayan shafin da miliyoyin mutane ke amfani da shi ya daina aiki na kusan tsawon sa’a biyu.

Yawancin ƴan Najeriya da ke amfani da shafin sun yi tunanin cewa a ƙasar ne kawai shafin ya daina aiki musamman a lokacin da suke zanga-zangar adawa da zaluncin ƴan sanda.

Tun ƙarfe 10 na daren Alhamis shafin ya daina aiki a Najeriya kuma matsalar ta shafi ƙasashe da dama.

Matsalar da Twitter ya samu ana ganin wani babban ƙalubale ne ga kamfanin, inda a ƴan kwanakin nan yake fuskantar suka da nuna ɓangaranci kan matakinsa na toshe wani rahoto da aka yi kan Joe Biden ɗan takarar jam’iyyar Democrat a zaɓen Amurka.

Tun da farko kamfanin ya sanar a Twitter cewa: “muna fuskantar matsaloli kuma babu wani alamu na yin kutse.”

Twitter ya ce sauyin tsari ne da aka yi kafin lokacin da aka tsara ya haifar da matsalar, wanda kuma ya shafi na’urarsa ta Intanet.

Rahotanni sun ce kunsan matsalar ta shafi dukkanin ƙasashen da ke amfani da Twitter.

Twitter ya taɓa daina aiki na tsawon sa’a ɗaya a 2019, haka ma a watan Fabrairun wannan shekarar.

Shafin kuma ya sha fama da koken kutse da ake yi wa shafukan manyan mutane inda a watan Yuli fitattun mutane a Amurka kamar tsohon shugaban ƙasa Barack Obama da shugaban Amazon Jeff Bezos da Bill Gates suka ce an yi wa shafinsu kutse

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku