Connect with us

Labari

Kamfanin Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora bidiyonsu a shafin

Published

on

Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora bidiyonsu a shafin

Kamfanin Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora bidiyonsu a shafin waɗanda ke zaune a wajen Amurka dangane da kuɗin da suka samu daga masu kallonsu a Amurka.

Kamfanin ya ce zai fara amfani da wannan tsarin ne daga watan Yunin 2021.

Haka kuma, Youtube ya bukaci masu ɗora bidiyonsu a shafin su mika bayanan harajinsu don tantance yawan kudin da za a rika fitarwa.

Kamfanin ya ce da zarar sun shigar da bayanansu, masu ɗora bidiyo za su riƙa ba da haraji tsakanin kashi 0 zuwa kashi 30 cikin ɗari kan duk wani kuɗi da suka samu daga masu kallo da ke zaune a Amurka.

Youtube ya ce kamfanin da ya fara kirkirar sa wato Google na da alhakin karɓar bayanan haraji da bai wa Hukumar Haraji rahoto idan mai saka bidiyo a shafin ya samu kuɗin shiga daga masu kallo a Amurka, karkashin dokar haraji ta kasar.

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku