Connect with us

Fasaha

Kamfanin Google yana Kokarin samar da Katin cirar kudi (Debit card)

Published

on

Katin Biyan Kudi na Google

Shahararren Kamfanin Fasahar Intanet na kasar Amurka (Google) yana Kokarin samar da Katin cirar kudi wato VISA Card. Wanda ake iya cirar kudi kamar katin ATM da dange-dangen su…

Wannan kati da kamfanin Google ke kokarin samarwa ya yi kama da na kamfanin Apple wato Apple Credit Card. Wanda shima ana amfani da shi wajan gudanar da harkokin kasuwanci, musamman a shafukan intanet.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin google ya fara gwajin aiki da sabon Katin cirar kudi da ya kera. Domin bada cikakkiya dama ga abokan huldar sa wajan gudanar da harkokin kasuwanci a tsarin zamani. Tuntuni wannan kamfani ya samar da manhajar biyan kudi mai suna Google Pay, wadda jama’a da dama ke amfani da ita wajan siye da siyarwa a intanet.

Haka kuma an bayyana cewa wannan cigaba zai amfanar da masu amfani da shi tare da manhajar Google Pay wajan bibiyar dukkanin harkokin cinikayyar da akayi da shi a shafukan intanet ko a manyan shaguna da kantina na zahiri kamar yadda ake amfani da katina wajan biyan kudin kaya da aka siya.

Bugu da kari mutum zai iya amfani da manhajar Google Pay wajan kulle catin saboda tsaro idan ya sulwanta, ma’ana ya 6ata ko aka sace. Amma har zuwa yanzu Kamfanin Google bai yiwa abokan huldar sa gwaggwaban tanadi ba ko garabasa ga dukkan mutanen da suka fara amfani da wannan sabon katin cirar kudi.

Kuma har zuwa yanzu kamfanin na Google bai fito ya bayyana ranar da zai kaddamar da fara aiki da wannan akti ba. Amma kamfanin yana ta kokari wajan kulla sabuwar alaaka da wasu manyan bankuna da kuma manyan cibiyoyin harkokin kasuwanci na kasar Amurka, domin karfafawa da bunkasa wannan kati har ya samu karbuwa a duniya baki daya.

Continue Reading