Connect with us

Fasaha

Karo na farko da za’a tura mace duniyar wata a 2024

Published

on

 

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (Nasa) ta bayyana shirinta na sake komawa Duniyar Wata nan da shekara ta 2024, wanda zai lashe kimanin Dala bliyan 28 ( $28bn) kwatankwacin famn biliyan 22 (£22bn) .

A daya daga bangaren shirin nata da aka yi wa laƙabi da Artemis, hukumar ta Nasa za ta aike da mace da namiji zuwa dandamalin Duniyar Watan, a sauka ta farko da za a yi da bil adama tun bayan shekara ta 1972.

Amma kuma shirin na wannan hukuma ya dogara ne ga sakin dala biliyan ($3.2bn) daga Majalisar Dokoki don fara gina tsarin dandamalin saukar.

‘Yan sama jannatin za su yi bulaguro a cikin wata silinda mai kama da Kumbo Apollo da aka yi wa laƙabi da Orion, wanda za a harba daga wata roka mai ƙarfi da ake kira SLS zuwa sararin samaniya.

Yayin da yake magana a yammacin ranar Litinin, shugaban hukumar ta Nasa Jim Bridenstine ya ce: “Dala biliyan 28 ($28bn) su ne kudaden da za a yi amfani da su a cikin shirin shekaru hudu masu zuwa na Artemis don sauka a kan Duniyar Watan.

”Tallafin kudaden rokar SLS, da na kumbon Orion, da kuma na tsarin saukar dan adam da ma rigunan sama jannatin- dukkannin abubuwan da suke cikin shirin Artemis na ciki.”

Amma kuma ya yi ƙarin hasken cewa: “Kasafin kudin da muka buƙata wanda yanzu haka yana gaban majalisar wakilai da ta dattawa sun hada da kimanin dala biliyamn uku da dubu dari biyu ($3.2bn) na shekara ta 2021 na tsarin saukar biladama.

”Yana da matukar muhimmanci cewa mun samu wadannan kudade ($3.2bn).”

Orion

Tuni dai ita Majalisar Wakilan Amurka ta amince da ƙudirin fitar da dala miliyan dari shida $600m don gina dandamalin sauka a Duniyar Watan.

Amma kuma Nasa za ta bukaci karin wasu kudaden don inganta Kumbon sosai.

Mr Bridenstine ya ƙara da cewa: “Ina son in yi karin haske, muna nuna matukar godiya ga Majalisar Dokoki cewa sun nuna yadda tallafawa tsarin saukar ke da matukar muhimmanci- wanda su ne za a yi amfani da dala miliyan dari shidan. Kana da gaske ne muna neman a ba mu cikakkun $3.2bn din.”

A watan Yulin shekara ta 2019, Mr Bridenstine ya shaidawa kafar yada labarai ta CNN cewa mace ‘yar sama jannati ta fako da za ta fara taka Duniyar Wata a shekara ta 2024 za ta kasance wacce ta taba tashi sama, wacce kuma daman take aiki a hukumar binciken sararin samaiya ta kasa da kasa”.

Ya kuma ce za ta kasance tana cikin tawagar ‘yan sama jannati ne.

A lokacin gudanar da wannan hira, akwai kimanin mata ‘yan sama jannati 12. Tuni suka hadu da sauran mata biyar ‘yan sama jannati na hukumar ta Nasa wadanda suka kammala horon da aka yi musu a cikin farkon wannan shekarar.

Amma har yanzu babu tabbaci ko za su iya cika ka’idojin tashi zuwa saman a kashin farko na sauka a cikin shekara ta 2024.

'Yan sama jannati na shekara ta 2017

‘Dalibai Yan sama jannati na baya-bayan nan sun hada da mata shida – biyar daga Nasa kana daya daga hukumar sararin samaniya ta kasar Canada

Bayan da aka tambaye shi game da lokacin da suka ɗiba na tantance ‘yan tawagar da za su tashi a cikin shirin na Artemis, shugaban hukumar ta Nasa ya ce yana fatan zaɓar tawagar ne akalla shekaru biyu kafin tashinsu na farko.

Amma kuma, ya ce: “Ina ga yana da muhimmanci mu fara gano tawagar Artemis tun da wuri … saboda ina ga zai zama wata hanya ta kara karfafa gwiwa.’

Sabuwar kasidar ta shata kashin farko na tsarin da suka hada da gwajin tashi a zagayen Duniyar Wata- da ake kira Artemis-1 a shekarar 2021.

Shugabar sashen da ke lura ta tashin biladama zuwa sararin samaniya a hukumar ta Kathy Lueders ta ce Artemis-1 zai kai har tsawon wata guda ana gudanar da gwaji kan muhimman abubuwa.

Ta ce gwajin tashin zai rage shiga hadri a cikin shirin Artemis-2, wanda zai maimaita bulaguron a zagayen Duniyar Watan tare da ‘yan sama jannatin.

An kuma kara sabon gwaji a cikin wannan shiri- nuna ayyukan yadda kumbon ke dosar sararin samaniya. Jim kadan bayan kumbo Orion ya rahu da kundun rokar SLS – wanda ake cewa matakin rura wutar da ke harba kumbon daga jikin rokar -‘yan sama jannatin za su tuka kumbom da hannu yayinda suke tunkara da kuma dawowa daga wannan mataki.

SLS leaves the launchpad

Wannan shi zai bayar da damar sarrafawa da gane ingancin kumbon na Orion, tare da ayyukan manahaja da injinan kumbon.

Artemis-3 kuma zai kasance shiri na farko da zai aike ƴan sama jannati zuwa duniyar wata tun bayan Apollo 17 shekara 48 da suka gabata.

Nasa ta ware dala miliyan 967 ga kamfanoni da dama don aiki a kan tsare-tsaren yadda saukar za ta kasance wajen kai su can.

Later in the decade, the plan calls for Nasa to establish a base for humans, called Artemis Base Camp, that would include the infrastructure needed for long-term exploration of the Moon.

Tushen Labarin

 

Continue Reading