Connect with us

Fasaha

Kasuwar Kudin Internet ta Fadi Kasa Warwas a Duniya – DFOnline

Published

on

darajar bitcoin ta faɗi a duniya

Kasuwar Crypto (kudin intanet) ta fadi kasa warwas, bayan darajar kudin mai matukar farin jini ta rikito da kashi 99 cikin 100, inda hakan ya yi awon gaba da wasu kudaden irin shi.

Darajar kudin intanet ta Terra Luna ta fadi daga kololuwar darajar dala 118, kwatankwacin naira 70,210 a watan da ya gabata, zuwa dala 0.09 a ranar Alhamis.

Wannan faduwa ta shafi darajar kudin intanet na TerraUSD, wanda a baya yake da darajar ba yabo ba fallasa.

Yawancin masu hannun jari da ke amfani da kudin sun fara janyewa daga manyan kamfanonin crypto, lamarin da ya sanya kasuwar tangal-tangal.

Cigaban labari

DUNIYAR FASAHA ONLINE –  #Kasuwar #Kudin #Internet #crypto #warwas #duniya

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku