Tun bayan da masana ilimi suka gano duniyar Pluto a shekarar 1930, kananan yara suka fara tasowa da tunanin cewa tsarin duniyoyin rana na da duniyoyi guda tara ne.

Hakan duka sun sauya a shekarar 1990, lokacin da masanan suka fara muhawara game da ko shin lallai Pluto ita ma duniya ce ko kuma tauraruwa.

A wani mataki mai cike da gagarumin ce-ce-ku-ce, kungiyar masu ilimin taurari ta yanke shawarar ba-zata a shekarar 2006 na lakaba wa Pluto suna ”gajeruwar duniya,” da hakan ya rage adadin yawan ainihin yawan duniyoyin zuwa takwas kawai.

Hakan ya biyo bayan ci gaba da karin bincike da masanan suka kara ƙaimi kan yiwiwar samun wata duniyar a tsarin duniyoyin, wato duniya ta tara bayan da aka bayyana wasu shaidun ilimin lissafin tabbatar da kasancewarta duniya a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2016.

A yanzu dai masanan suna da shaidu game da kasancewar Pluto din a matsayin duniya.

Fasalin duniyoyin

Tsarin duniyoyin rana

Bayanan hoto: Zanen tsarin duniyoyinmu na rana – Asalin hoton, NASA/Jet propulsion Laboratory- Caltech

Fasalin jerin duniyoyin a kan tsarin duniyar rana, da ya fara da wadanda suka fi kusa da rana har ya zuwa nesa da ita sun hada da duniyoyin: Mercury da Venus da Earth da Mars da Saturn da Uranus da Neptune da kuma duniya ta tara da aka dade ana tababa a kai, wato Pluto.

Masana sun bayyana cewa manyan duniyoyi da ke kusa da rana — Mercury da Venus da Earth da kuma Mars — ana kiran su da suna “duniyoyi masu ƙunshe da manyan abubuwa” saboda sararinsu na kunshe da duwatsu.

Pluto ita ma tana da duwatsu, baya ya daskararriyar kankara da ke samanta, amma ba a taba kamanta ta da wadannan duniyoyi hudu ba.

Kana manyan duniyoyi hudu da suka fi nesa da duniyoyin wajen kusa da rana— Jupiter da Saturn da Uranus da kuma Neptune — su kuma a kan kira su da laƙabin “masu kama da Jupiter” saboda girmansu da ke da kamanni da na wadancan duniyoyi hudu na farko.

Yanzu dai ga wasu takaitattun bayanai game da gawartattun duniyoyin takwas da tabbas suna nan, sun kuma fara da mafi kusanci da rana ya zuwa tunkarar wajen nesa da ranar – kana akwai bayani game da Pluto da masanan suka yi wa laƙabi da ‘gajeriyar duniya’, bayan tabbatar da ita a matsayin duniya sakamakon wasu bincike da kuma shaidu da suka gabatar game da ita:

1. Mercury

Duniyar Mercury

Bayanan hoto: Launukan na nuna yanayin duwatsun sararin duniyar Mercury daban-daban – Asalin hoton, NASA

Baya ga kasancewa duniya mafi kusa da rana, Mercury ita ce duniya mafi kankanta a cikin duniyoyi.

Saboda kusancinta da rana, Mercury kan fuskanci yawan sauye-sauye a yanayin ma’aunin zafi ko sanyi na dare da rana: Da rana, zafin kan yi tsanani zuwa ma’aunin 840 F (450 C), yanayin zafin ya kai yadda zai iya narkar da dalma.

Kuma da dare yanayin kan sauka zuwa ma’aunin 290 F (kasa da 180 C).

Mercury na da yanayin mai ƙanƙanta na iskar shaka ta oxygen, da sodium, da hydrogen, da helium da kuma ba za su iya tarwatsa ɓaraguzan duwatsun da ke yawo a duniyar sama ba.

Hakan ne ya sa sararin duniyar ke mamaye da ramuka kamar na duniyar wata, wanda wata shaida ce da ke nuna cewa duniyar ta Mercury na da tarihin yawan yin taho mu gama da dandazon fasassun taurari.

Ko shakka babu, binciken da masana suka gudanar game da sararin kan duniyar Mercury a shekarar 2016, ya nuna cewa duniyar ka iya ci gaba da samun girgizar kasa ko kuma a ce ”girgizar Mecury”.

Hakan na nufin cewa duniyarmu ta Earth ko duniyar kasa ba ita kadai ce ke fama da irin wadannan abubuwa ba.

Haka kuma, a baya saman duniyar Mercury ya sha sauya fasali saboda yawan aman wutar dutse.

Amma kuma, wani bincike na shekarar 2016 ya nuna cewa akwai yiwuwar yawan aman wutar dutsen a duniyar Mercury ya kawo karshe a cikin kusan shekaru biliyan uku da rabi da suka wuce.

2.Venus

Duniyar Venus

Bayanan hoto: Yanayin zafin saman duniyar Venus yawanci ya kan wuce ma’aunin 700 kelvins, zafin da zai iya narkar da dalma – Asalin hoton, Ssv/Mipl/Magellan/Nasa

Venus ita ce duniya ta biyu daga cikin tsarin duniyar rana, kuma girmanta kamar na duniyar Earth da muke ciki ce.

Wasu hotunan da aka dauka ta hanyar tauraron dan adam ta kasan yanayin tsarinta, ya nuna cewa sararinta na da tsaunuka da kuma manyan duwatsu masu fitar da wuta.

Amma baya ga haka, duniyoyin biyu ba su da wata sauran kamanceceniya.

Saboda yanayin gurbatacciya iskar da ke cikinta wacce ta kunshi gajimare mai kauri na sinadarin sulfuric acid, duniyar Venus kamar kwatankwacin yadda masana’antu ke fitar da gurbatacciyar iska ce.

Tana da tsananin zafi fiye ma da duniyar Mercury.

Yanayin ma’aunin zafin sararin duniyar Venus ya kai 900 F (465 C), wacce karfin zafinta kan iya ragargaza tare da hallaka duk wata halitta.

Kana wani abin mamaki, Venus na zagayawa sannu a hankali ne daga gabas zuwa yamma, hanyar da ke daura da akasarin sauran duniyoyi.

Masana sun yi amanna cewa duniyar Venus na da abubuwa kashi biyu — daya a sararin sama da safe, daya kuma da yammaci.

Saboda ta kan kasance mafi haske cikin duk wani abu da yake sama.

3. Earth (duniyar kasa)

Duniyar Earth

Bayanan hoto: Mutane sama da biliyan bakwai ne ke zaune a nan (ba za a iya gani ba) – Asalin hoton, Nasa/Dscovr

Duniyar Earth ko kuma duniyar kasa ita ce ta uku daga duniyar rana, kuma cike take da ruwa, inda biyu bisa ukun duniyar a kewaye yake da teku.

Ita ce kuma duniya ta biyar mafi girma cikin duniyoyin.

Ita kadai ce duniyar da ke bai wa halittu damar rayuwa ya zuwa tsawon lokaci, kuma a cikinta muke rayuwa.

Kana yanayin duniyar Earth na da nagartattun iskar nitrogen da kuma oxygen.

Amma kusan kashi biyar na iskar shaka ta oxygen da ke sararin duniya itatuwa ne ke samar da su.

Yanayin sararin duniyar Earth na da kashi 78 bisa dari na iskar nitrogen da kashi 21 bisa 100 na iskar shaka ta oxygen, da kuma ɓurɓushin ruwa, da iskar carbon dioxide da sauran wasu iskar gas.

Babu wata duniya a cikin tsarin duniyoyinmu da suke da tarin iskar oxygen kyauta wacce ke da matukar muhimmanci ga rayuwa kamar na duniyarmu ta Earth ba.

Earth na juyawa a kan layinta a kan kafa 1,532 kan kowace daƙiƙa (mitoci 467 kan ko wace dakika).

Duniyar kan kewaya kusa da rana kan fiye da mil 18 kan kowace daƙiƙa (kilomita 29 kan kowace daƙiƙa).

Tana da fadin diameter kusan mil 8,000 (kilomita 13,000 ) kuma fasalinta a zayage take.

Sai dai za a iya cewa ba ta kai kamar fasalinta bai zagaye sosai kamar ƙwallo ba.

Kusan kashi 71 bisa 100 na sararin duniya kewaye yake da ruwa, kuma galibi yana cikin tekuna ne.

4. Mars

Duniyar Mars

Bayanan hoto: Za a iya danganta bakaken jirwayen da ke saman duniyar Mars da kwanciya da gudanar ruwa a wurin – Asalin hoton, NASA

Mars ita ce duniya ta hudu daga tsarin duniyar rana, kuma tana da sanyi, kana tana kama da hamada saboda kewaye take da kura.

Kurar ta samo asali ne daga wasu burbushin baƙaƙen ƙarafuna, da kan bai wa duniyar wasu irin fitattun launukan jan.

Duniyar Mars na da yanayi irin na duniyar Earth: Tana da duwatsu, tana ta tsaunuka, da tuddai da kwari, kana tana da guguwa da suka hada da ta kura da mahaukaciyar iskar guguwa da ambaliyar teku.

Wata sahihiyar shaida ta kimiyya ta nuna cewa a cikin biliyoyin shekarun da suka gabata ta fi kasancewa duniya mai dumi, da damshi sosai.

Akwai alamun cewa an taɓa samun tekuna da koguna a ciki.

Duk da cewa duniyar ta Mars yanayinta ba shi da ƙarfin rike ruwan da zai kwanta a kai har na tsawon lokaci, amma har yanzu akwai alamun gurbin kwanciyar ruwa a yanzu haka.

A cikin watan Yulin shekarar 2018, masana kimiyya sun bayyana cewa sun gano shaidar ruwan tafki a saman kudancin kusurwar mai ƙanƙara.

Irin waɗannan bayanai da ke fitowa a game da duniyar Mars ne ya sa hankulan masu binciken sararin samaniya ke ƙara ƙaimi wajen fuskantar ta, da hakan ta sa Mars din ta zama duniyar da aka fi bincike a kai a cikin duku duniyoyin da ke kan tsarin duniyar rana.

5. Jupiter

Duniyar Jupiter

Bayanan hoto: A cikin kusan mil 89,000 , duniyar Jupiter za ta iya hadiye duniyar Earth 1,000 – Asalin hoton, Nasa/Damian Peach

Duniya ta biyar daga duniyar rana, Jupiter babbar duniyar iskar gas ce, kuma mafi girma a tsarin duniyarmu ta rana — fiye da ninki biyu kamar idan aka hade duka duniyoyin, kamar yadda hukumar binciken sararin samaniya NASA ta bayyana.

Gajimaren da ke yawo suna da launuka da dama saboda ɓurɓushin launukan iskar gas daban-daban. Kana babban abin da aka fi gani a gajimaren nata shi ne wata ƙatuwar guguwa mai fadin mil 10,000 da ake kira ‘Great Red Spot’.

Jupiter duniya ce mai gawurtaccen sarari mai ƙarfin maganadisu, kuma tana dan kama da karamin tsarin duniyar rana.

Yanayi sararin Jupiter na kama da na rana, da akasari ke kunshe da iskar gas ta hydrogen da helium.

Hasken wuta mai launuka da bakaken layikan da suke kewaye da duniyar Jupiter sun samo asali ne daga gagarumar iskar gabashi zuwa yammaci a saman duniyar da ke gudun fiye da mita 335 cikin kowace sa’a.

Fararen gajimare a yankuna masu haske su kuma sun samo asali ne daga burbushin daskararren sinadarin ammonia, yayin da bakaken gajimaren su kuma suka samo asali daga sauran sinadarai da ake samu daga bakaken damarar da ke kewaye da duniyar.

A wasu lokutan kuma a kan samu shuɗayen gajimare.

6. Saturn

Duniyar Saturn

Bayanan hoto: Zobunan duniyar Saturn na kunshe da kurar ruwan kankara – Asalin hoton, Nasa/Ames/SwRI

 

Saturn ita ce duniya ta shida daga tsarin na duniyoyin rana. An kuma fi sanin ta da kasancewa mai zobe.

Lokacin da masanin kimiyya Galileo Galilei ya fara bincike kan duniyar Saturn a farkon shekarar 1600s, ya dauka wani dan abu ne mai ɓangarori uku: wato duniya da kuma wasu manyan duniyoyin wata a sauran gefenta.

Ba tare da ya san cewa ya yi tozali da duniya mai zobuna ba ce, mai ilimin taurarin sai ya fara karamin zane — na alamar wata babbar da’ira da wasu kananan biyu — a cikin dan littafinsa, yana bayyana abin da ya gano.

Shekaru 40 bayan nan, Christiaan Huygens ya bayyana cewa zobuna ne.

Zobunan kamar an yi su ne da kankara da kuma duwatsu kana masana kimiyya sun kasa gano yadda aka yi suka kasance a haka.

Duniyar mai iskar gas, akasari tana kunshe da iskar hydrogen da helium ne, kana tana da wata da dama.

7. Uranus

Duniyar Uranus

Bayanan hoto: Mai ilimin taurari William ne ya gano duniyar Uranus a shekarar 1781 – Asalin hoton, NASA

Duniyar Uranus wacce ita ce ta bakwai a tasrin duniyoyin tara da gajimare mai kunshe da iskar hydrogen sulfide, sinadarin da ya fike sama rubabben kwai doyi. Tana juyawa daga gabas zuwa yamma kamar duniyar Venus.

Amma ba kamar Venus ko kuma sauran duniyoyi ba, layin ekweta dinta na kusan daidai da kusurwar daman inda ta karkata ne — galibi kuma ta kan karkata ne a gefenta.

Masu iimin taurari sun yi amanna cewa wani abu da ya ninka duniyar Earth girma sau biyu ne ya yi taho mu gama da duniyar Uranus ne shekaru biliyan 40 da suka wuce, yake sa Uranus din tana karkacewa.

Wannan karkacewar na haifar da yanayi masu tsanani da kan kai shekaru 20 ko fi.

Ana kuma hasashen taho-mu -gamar ta fasa duwatsu da kankara cikin hanyar duniyar ta Uranus. Hakan daga bisani ya haifar da duniyoyin wata 27.

Sinadarin Methane da ke kunshe ya kara bai wa duniyar Uranus shudi da koren launi. Tana kuma da zobuna 13 masu koɗaɗɗen launi.

8. Neptune

Duniyar Neptune

Bayanan hoto: Neptune ita ce duniya mafi girma a kan tsarin duniyoyin rana, kana kimanin duniyar Earth 60 za su iya zama ciki – Asalin hoton, NASA

 

Neptune ita ce duniya ta takwas daga jerin duniyoyin rana, kuma girmanta ya kusa da na duniyar Uranus, kuma an san ta da wani irin yanayin iska mai karfin gaske.

Duniyar Neptune a fili take ga kuma dan karen sanyi.

Duniyar na da girman da ya ninka har fiye da sau 30 idan aka kwatanta daga duniyar rana zuwa duniyarmu ta Earth.

Neptune ita ce duniya ta farko da aka yi hasashen cewa tana nan ta hanyar amfani da ilimin lissafi, kafin ma a gano ta da ido.

Wani mai ilimin taurari dan kasar Jamus Johann Galle ya yi amfani da lissafi wajen gano duniyar Neptune a madubin hangen nesa.

Neptune tana da girman da ya linka har sau 17 kamar girman duniyar Earth kuma tana da tsakiya ma duwatsu.

9. Pluto (gejeriyar duniya)

Duniyar Pluto

Bayanan hoto: Masana sun dade suna takaddama kan Pluto ko duniya ce ko kuma tauraruwa inda daga bisani aka yi mata lakabi da ‘gajeriyar duniya’ – Asalin hoton, Caltech/R. Hurt (IPAC)

Kasancewarta duniya ta tara daga cikin tsarin duniyar rana, Pluto ta bambanta da sauran duniyoyin ta ko ina.

Tana da ƙanƙanta fiye da watan duniyar Earth; yanayin yadda take zagayawa kamar fasalin ƙwan kaza ne, tana yi tana faɗa wa cikin hanyar zagayen duniyar Neptune; kana zagayen duniyar Pluto bai cika fadawa a kan hanya daya kamar sauran duniyoyin ba — a maimakon haka, ta kan zagaya a bisa awon kusurwar 17.1 sama ko kasa.

Daga shekarar 1979 har ya zuwa farkon shekarar 1999, Pluto ta kasance ita ce duniya ta takwas daga jerin duniyar rana.

Daga bisani a ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 1999, ta tsallaka hanyar duniyar Neptune, kana ta ƙara zama mafi nisa daga cikin duniyoyin — har sai da aka sake yi mata laƙabi da wada ko kuma gajeriyar duniya.

Tana da sanyi, ga kuma duwatsu da wani irin yanayi mai rashin tabbas da ka iya sauyawa a babu zato ba tsammani.

Pluto duniya ce kewaye da kankara, da tsaunuka masu kankara, ga kuma sinadaren methane da ammonia kewaye da ita.

Tushen Labari