Connect with us

Fasaha

Bambancin dake tsakanin gidan rediyon AM da FM?

Published

on

rediyon AM da FM

Bambancin dake tsakanin gidan rediyon AM da FM?

Wannan batu yanada fa’ida a tsakanin al’umma kamar yadda aka bukaci a bayani akan bambanbcin dake tsakanin su, duba da yadda rediyo take da matukar muhimmanci a rayuwar mu. Tabbas rediyo tana da matukar muhimmanci a rayuwar mu ta yau da kullum. Idan muka kalli yadda fasaha take canza abubuwa masu yawa ta fuskoki daban-daban kama daga kere-kere har zuwa sabunta tsofaffin na’urori.

Daga cikin al’amuran fasaha na farko har zuwa wannan lokacin, zamu ga cewa fasahar rediyo tana taka muhimmiyar rawa a fadin duniya baki daya. Duba da yadda ta zamo hanyar yadawa da sauraron al’amura masu yawan gaske kama daga Labaran Duniya, Ilmanatarwa, Fadakarwa har ma da Nishadantarwa.

A bangaren fasaha, rediyo ta zamanto hanyar babba wajan sadarwa ko isar da sakonni cikin sauti ko murya. Domin idan muka kalli fasahar waya (Telephone) zamu ga shima asalin sa a kan tsarin rediyo yake tafiya wajan sadarwa ko isar da sakon sauti daga wani bangare zuwa wani bangare na duniya.

Idan muka dawo kan batun bambancin dake tsakanin tsarin yada shirye-shirye na kafafen rediyo wato AM da FM, zamu ga cewa kusan bambancin su duk abayyane yake kamar yadda na tsara su a kasa;

Rediyo Tsarin AM

Rediyo Tsarin FM

Nisan zango daga 535 zuwa 1705 kHz Gajeren Zango daga 88 zuwa 108 MHz
Rashin Kyawun Sauti Ingantaccen Sauti Tartar
Saukin Kamuwa da hayaniya, tsawa da walkiya Baya kamuwa da hayaniyar tsawa ko walkiya
Anyi nasarar fara aiki da shi a shekarar 1970 An kirkiro shi a shekara 1930

Da akwai bayanai masu yawa akan bambancin dake tsakanin su, amma wadancan sune mafi saukin fahimta. Bugu da kari, idan muka kalli yadda ake bude gidajen rediyo akai-akai musamman a wannan jahar ta mu (Kano), zamu ga cewa mafiyawancin su na FM ne domin sunfi saukin budewa akn gidan rediyon AM. Hakan yana nuni da cewa gidan rediyo tsarin AM yana da tsada matuka, domin kusan zamu ga cewa Gwamnati ce take iya daukar nauyin bude gidan rediyon AM. Misali anan Kano Gidan Rediyo na farko wanda shi aka fara sani, Gwamnatin Jahara Kano ce ta kafa shi. Kuma har yanzu shi kadai ne akan tsarin AM. Duk sababbin da suka biyo baya masu zaman kansu ne kuma suna kan tsarin FM ne. Saboda haka Gidan Rediyo Kano ya zamo uwa ma ba da mama.

Da wadannan bayanai nake fatan Allah ya fahimtar da mu baki daya.