Connect with us

Featured

Kotu ta tilasta wata kaka goge hotunan jikokinta a Facebook

Published

on

Shafin Facebook

Wata kotu a ƙasar Netherlands ta yanke hukuncin cewa wata mata ta goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta na Facebook da Pinterest ba tare da izinin mahaifansu ba.

Lamarin ya kai ga kotu ne bayan matar ta samu saɓani da ‘yarta.

Kotun ta yanke hukuncin cewa batun yana cikin iyakar Ƙa’idar Kare Bayanai ta Tarayyar Turai (EU’s General Data Protection Regulation).

Wani ƙwararre ya ce hukuncin manuniya ce kan “matsayin da Kotun Turai ta ɗauka tsawon shekaru game da kare bayanan mutum”.

Maganar ta je gaban kotu ne bayan matar ta ƙi goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Cigaban Labari

Continue Reading