Connect with us

Fasaha

Ma’ana da Muhimmancin Hacking a Duniyar Fasaha

Published

on

Ma'ana da Muhimmancin Hacking a Duniyar Fasaha

Ma’ana da Muhimmancin Hacking a Duniyar Fasaha

Wannan batu ne da kusan kullum sai an tattauna akansa a kafafen sadarwa na intanet da na yada labarai. Bukatar amfani da intanet kullum kara habbaka takeyi a tsarin gudanar da al’amuran rayauwar yau da kullum. Haka zalika kullum ana kara karfin matakan tsaro na intanet domin magance aiyukan ta’addancin da ke faruwa akai akai a fadin duniya baki daya.

Menene hacking?

Kalmar hacking tana nufin amfani da kololuwar ilimin fasaha musamman na sarrafa kwamfuta, tsarin bada umarni na kwamfuta (programming) da sauran su… domin warware wasu matsaloli ko gudanar da aiyuka na musamman. Ta wata fuskar kuma, hacking yana iya zama aiyukan ta’addanci da ake gudanarwa a intanet kama daga kutse, datsar hanyar sadarwa, damfara, yada miyagun manhajoji domin cutar da na’urori da dabi’ar satar bayanan sirri da sauran su… wadanda kullum sake salo suke yi domin gano baraka a shafukan intanet da manhajoji musamman wadanada ke kunshe da bayanan sirri na gwamnati ko na wasu kusoshi a duniya, harkokin kasuwanci, da na hadahadar kudade. A wani bangaren kuma akwai hacking da akeyi mai amfani da muhimmanci wanda yakan zamo babbar sana’a ga wanda ke gudanar da shi, saboda babu laifi wajan aikata shi wato ethical hacking.

Waye hacker?

Kalmar hacker ta na nufin kwararre, kuma masanin sirrin sarrafa Kwamfuta, wanda yakan bi wasu hanyoyi na daban wajan sauya dabi’ar kwamfuta domin cimma wata manufa tasa, ko kuma warware matsaloli masu sarkakiya. Kuma za’a iya fahimtar sa da wanda yake gudanar da aikin ta’addanci a intanet. Amma fa ba duk hacker ne yake aikin ta’addanci ba. Akwai wadanda suke aiki mai kyau (ethical hacker).

Ire-iren Hackers a Duniyar fasaha

A duniyar fasaha akanyi amfani da launika (Colours) wajan bambance tsakanin su. Kuma launin yana da ma’ana sosai wajan bayyana aiyukan su ta yadda kowa zai fahimta.

  • White hat hacker: An nufin hacker mai farar  malafa. Kuma wannan nau’i na hacker abin so ne kwarai a cikin al’umma, domin dukkan aiyukansa na gyara ne (ethical hacking). Shi white Hat Hacker yana amfani da iliminsa wajan gano baraka (backdoor) wadda za aiya yin kutse, kuma ya toshe ta. Yana gudanar da ikinsa na hacking a bisa yarjejeniya tsakanin sa da wanda ke bukatar sanin karfin matakin tsaron kamfanin sa ko wata manhaja ke da shi domin kaucewa kutsen ‘yan ta’adda. Kuma ana biyansa albashi mai tsoka.
  • Black Hat hacker: Shi kuma wannan nau’in ya kasance dan ta’addan intanet na hakika wanda ke amfani da karfin ilimnsa wajan yin kutse ga hanyoyin sadarwa da kuma rusa dukkan matakan tsaro domin cimma mummunar manufarsa ta satar bayanan sirri da kuma kirkirar gurbatattun manhajoji, da yada su a intanet da kwamfutoci domin samun damar cutar da da jama’a masu ma’ammali da na’urori da intanet (non-ethical hacker). Wanda sunan sa ya bayyana aikinsa, baya bukatar izini ko umarni, kuma shi ne mafi illa daga cikin hackers a duniyar fasaha.
  • Gray Hat hacker: shi kuma wannan nau’in hacker, ya hada dukkan dabi’un White hat hacker da na Black hat hacker wajan gudanar da aikinsa na kutse. Yana amfani da fasahar sa wajan binciko baraka, batare da neman izini ko sahalewar mai kamfani ba, idan ya gano baraka, zai sanar da mai kamfani ko manhaja. Sannan ya nemi da biya shi wasu kudade domin ya toshe barakar da ya gano. Idan aka ki bashi kulawa, sai ya yada dukkan sirrin shafin ko manhajar a intanet domin kowa ya gani, wanda hakan ka’iya zama barazana ga kamfani ko manhaja. Idan aka bi tsarinsa za’a zauna lafiya. Shi da haka yake nema kudi a koda yaushe.
  • Red Hat Hacker: Shi kuma wannan, mai jar malafa yana gudanar da aikinsa kamar na farko mai farar malafa domin magancewa ko dakile aiyukan ‘yan ta’addan intanet wato masu bakar malafa. Yana aiki kamar hukuma ne. Yana daukar doka a hannunsa. Yana gudanar da aikinsa ba tareda sani ko iznin masu kamfani ko manhaja ba. Yana yakar black hat hackers, yana tarwatsa aiyukan su da na’urorin su a duk lokacin da yaso yakar su. Wannan nau’i na hacker yana daga cikin rukunin hackers mafi fahimta, kwarewa da gogewa a wannan fanni kusan fiye da kowa.

Da wadanan takaitattun bayanai nake karawa dalibai masu nazari a fannin kimiyyar kwamfuta (Computer science) da cewa, lallai su dage wajan zama daya daga cikin masu gudanar da aiyuka nagari a ko’ina kuma a kowanne lokaci. Idan mutum yana son ya dade yana gudanar da al’amuran sa a intanet ba tareda shiga matsala ko rudani ba, lallai ya aikata gaskiya, ya kuma kasance mai rikon amana da boye sirrin abokan huldar sa na intanet. Idan mutum yabi gurbatacciyar hanya wajan gudanar da mu’amalolin sa a intanet, to fa komai daren dadewa za’a gano shi kuma za’a kama shi. Sannan a hukunta shi. Saboda haka idan kunne yaji, jiki ya tsira.

Insha Allahu bayan Sallah zanyi programme kaitsaye akan wannan batu.