Connect with us

Fasaha

Ma’anar Cloud Computing da Amfaninsa

Published

on

Ma anar cloud computing da amfaninsa

Cloud Computing tsari ne na fasaha da ake amfani da shi cikin sani ko rashin sani, a bangarori masu yawa na intanet.

Wannan fasaha ta cloud computing ba sabuwa bace, sai dai a kowanne lokaci ana sabunta dukkan tsare-tsaren da ta ke tafiya akai domin saukakawa da kuma ingantawa ga masu amfana da wannan fasaha a fadin duniya baki daya.

Kalmar ‘cloud’ a harshen hausa tana nufin girgije, gizagizai ko gajimare. Amma a tsarin fasaha tana nufin hadaka tsakanin sassan na’urori wato Hardware da kuma Software wato manhaja masu yawan gaske, wajan gudanar da aiyuka tare domin samar da cikakke kuma gamsashshen sakamakon aiki ga Al’umma masu ta’ammali da kafofin intanet a fadin duniya baki daya.

Cloud computing yana bayyana amfanin hardware da software a babban matakin sadarwa na intanet. Da wannan tsari kowa yana da damar sarrafa dukkanin aikace-aikace ko ajiyewa da daukar aiyuka (files) da ke intanet ta hanyar amfani da na’urorin zamanai (computer da smartphones).

Wannan fasaha ko tsari na cloud computing kusan dukkan masu amfani da intanet suna amfana dashi cikin sani ko rashin sani. Domin idan mutum yana amfani da Google musamman email (Gmail), zai iya amfana da abubuwa masu yawa har da manhajoji daga sassan google ta hanyar amfani da dukkan na’urori masu alaaka da intanet daga ko’ina cikin fadin duniya.

Masu amfani da email suna iya adana kayayyaki kamar; Litattafai, sauti, fayafayan bidiyo, manhajoji da sauran su duk acikin akwatin sakonnin email. Bayan haka akwai shafukan intanet na musamman da suke siyar da guraben adana kayan aiki da sauran su. Kuma sukan bada damar ajiya a kyauta wato free cloud storage. A duk lokaci da ake da bukatar gurbin a jiya na cloud, za’a iya zabar iya adadin giraman storage da ake da bukata.

Kuma wannan fasaha ta cloud computing tana tafiya ne akan tsarin Virtualisation wanda har kullum wajan bayani akan kowanne dayan su baya cika ba tareda an ambace su gaba daya ba.

Cloud computing ya zamo babban ginshiki a duniyar fasaha ta intanet domin manyan kamfanoni masu gudanar da aiyukan su a intanet sun dogara dashi. Haka kuma manyan cibiyoyi masu mu’amala da na’urori da kuma bukatara adana aiyukan su a babbar na’urar adana kayan aikai (server) suma suna amfani da wannan tsari. Haka kananan matakai na yadda mutane ke ajiye files a Gmail, Goolge drive, google photos  da sauran su… duk misali ne na cloud storage. kuma ba kamfanin google ne kadai yake bada ire-iren wadannan aiyuka ba, akwai kamfanoni masu yawan da baza su kirgu ba suma suna bada wadannan services na cloud a intanet. Akwai free da kuma wadanda sai an biya kudi.

Bugu da kari, tsarin yadda ake tsara shafukan intanet, suma akwai cibiyoyin intanet masu bada guraben adana shafukan intanet (Web Hosting services) suma suna amfani da wannan tsari na cloud. Manyan ma’ajiyar sirrin abokan hulda na bankuna suma suna amfani da tsarin cloud wajan adana komai na su.

Kuma wannan tsari na cloud computing, ba a tattare yake waje daya ba. A ko ina za a iya samar dashi kama daga; kamfanoni suma zasu iya samar da nasu, manyan jami’o’i suma zasu iya samra da nasu, manyan cibiyoyin bincike, bankuna, manyan cibiyoyin kasuwanci da sauran su kowa zai iya kaddamar da na sa cloud system daidai da bukatar sa. Haka zalika kamfanoni zamani suna iya amfani da cloud computing wajan gudanar da dukkan aiyukan su akan tsarin cloud ba tareda amafani da dakunan ofis-ofis na zahiri ba. Dungurugum za a iya gudanar da dukkan aiyukan ofis a cloud system.

Dafatan Allah ya amfanar damu a cikin wannan al’amari baki daya.

Continue Reading