Connect with us

Fasaha

Ma’anar .com, .org, .net da sauran su a shafukan intanet

Published

on

karshen adreshin intanet tlds

Ma’anar .com, .org, .net da sauran su a shafukan intanet

Wadannan abubuwa suna da matukar muhimmanci a cikin al’amuran intanet. Kuma kowanne yana kunshe da ma’anarsa, kuma sukan bayyana a karshen kowanne adreshi na intanet bayan digo [.] wanda ake kira dot. Ana kiran su da harshen turanci “TLDs”. Misali https://duniyarfasahaonline.com a cikin wannan adreshin .com ake nufi da TLD.

Muna haduwa da nau’i-nau’i na wadannan al’amura (TLD) a mu’amalar mu ta intanet. Domin dukkan shafukan da muke ziyarta suna da adreshi kuma tld dinsu yakan sha bam-bam da juna, duba da tsari ko abubuwanda aka gina shafin akan sa. Wanda ma’anar tld tana ta’allaka da manufar shafin.

Bugu da kari, cibiyar dake kula da dukkanin adreshin shafukan intanet ta duniya (ICANN) wadda ita ce kanwa uwar gami tsakanin adreshin intanet (Domain) da kuma lambobin sirri na sadarwa tsakanin na’urori (IP address), ta kasa tsarin TLD gida biyu kamar haka; akwai wadanda suke akan tsarin standard wadan aka fi sanin su duk duniya (Generic TLDs) da kuma wadanda ake alaakan ta su da sunan kasashen dake amfani da su (Country-specific TLDs).

Ga misalan TLD da ma’anar su

Kashi na farko (Generic TLDs)

TLDs Ma’anar Su
.COM Shafin Kasuwanci (Commercial Business)
.ORG Shafin Ma’aikatu (Organisations)
.NET Shafin cibiyoyin Intanet (Network Organisation)
.EDU Shafukan Cibiyoyin Ilimi (Educational facilities) kamar Jami’o’i
.GOV Shafukan Gwamnati (Government agencies)
.MIL Shafukan Soji (Military)
.BIZ Shima ana amfani da shi a Shafukan Kasuwanci
.INFO Wannan yanada alaaka da shafuka na cibiyoyin ma’adanar bayanai a intanet (Informative Internet Resouces)

da sauran su…

Kashi na biyu (Country-specific TLDs)

  • .NG
  • .COM.NG
  • .ORG.NG
  • .GOV.NG
  • .EDU.NG

A cikin wadannan zamu ga cewa kowannen su yana kunshe da ma’anar sa ta asali sannan kuma sun bayyana kasar da aka yi musu rijista wato Najeriya (Nigeria, NG). Kuma kowacce kasa tana iya tsara nata da sunan kasarta a karshe.

Haka zalika akwai wasu guda hudu (4) da ake amfani da su wajan bada misali kadai, amma ba shafukan intanet dake aiki ba. kamar su;

  • .example — Ana amfani da shi kawai domin bada misali.
  • .invalid — An amfani da shi kawai ga adreshin da baya aiki.
  • .localhost — Wannan ana amfani da shi a kan Na’ura Kwamfutar da babu intanet akan ta.
  • .test — Ana amfani da wannan domin gwaji kawai
Continue Reading