Connect with us

Featured

Mai kuɗin duniya zai sauka daga shugabancin Amazon

Published

on

https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55918607

Wanda ya kafa katafaren kamfanin sayar da kayan nan a shafin intanet Amazon a shekara 30 da suka gabata Jeff Bezos, zai sauka daga muƙaminsa na jagoran kamfanin.

Zai koma ya zama shugaba mai cikakken iko, matakin da ya ce zai ba shi “lokaci da karsashi” wajen mayar da hankali kan sauran ayyuka.

Andy Jassy, wanda ke jagorantar bangaren kasuwancin na’urori masu ƙwaƙwalwa da shafin yanar gizo na kamfanin ne zai maye gurbin Mr Bezos.

Za a samu sauyin ne a tsakiyar shekarar 2021, in ji kamfanin.

“A matsayina na babban jagoran kamfanin Amazon, jan aiki ne kuma mai cinye lokaci. Idan kana da gagarumin daukar nauyi irin wannan, yana da wahala ka mayar da hankalinka kan wani abu daban,” kamar Mr Bezos ya bayyana a cikin wata wasika da ya rubuta wa ma’aikatan kamfanin na Amazon ranar Talata.

“Shugaba mai cikakken iko zan kasance ina gudanar da aikina a bangaren muhimman yunkurin ayyukan Amazon, amma zan kuma samu lokacin karsashin da nake bukata don mayar da hankali kan ayyukan da nake begen yi kamar su ”Day 1 Fund”, da ”Bezos

“Ban taba samun karin karsashi ba, kuma ba wai game da yin murabus bane, Ina matukar kaunar ganin ci gaban da nake ganin kamfanin zai kara samu,” ya kara cewa.

Shahara a shafukan sada zumunta

Mr Bezos, mai shekaru 57, ya jagoranci kamfanin na Amazon tun bayan kafa shi a matsayin kantin sayar da litattafai ta shafin yanar gizo a shekarar 1994.

Yanzu kamfanin na da ma’aikata miliyan daya da dubu dari uku a fadin duniya, kuma suna gudanar da ayyukan rarraba rarraba kayyaki ga wadanda suka saya daga kamfanin, da tallace-tallace da tsara faye-fayen bidiyo da sauransu.

Ya samu gagarumin nasibin dala biliyan dari da casa’in da shida da miliyam dari biyu, kamar yadda hukumar tantance jerin sunayen attajiran duniya Forbes ta bayyana.

Kamfanin ya riga ya shaida babbar bunkasa a shekarar da ta gabata, yayin da annobar korona ta haifar da yawan sayen kaya da shafukan intanet.

Andy Jassy
Andy Jassy ya kasance a Amazon tun a shekarar 1997

Kamfanin ya bayyana samun ribar dala biliyan dari uku da tamanin da shida ($386bn) kwatankwacin fan biliyan dari biyu da tamanin da uku (£283bn) a cinikinsa na shekarar 2020, karin kasha 38 bisa dari (38%) daga shekarar 2019. Ribar ta kusan linkawa, bayan da ta hau zuwa dala biliyan ashirin da daya da miliyan dari uku.

Yayin da yake sanar da tsare-tsaren, Mr Bezos ya ce zai cigaba da mayar da hankali kan sabbin kayyaki da kuma yunkuri.

“Idan kuma duba sakamako game da kudaden shigarmu, abin da za ka ainihin gani su ne sakamakon da suka tattaru na abubuwan da muka ƙirƙira. Yanzu haka ina kallon Amazon a matsayin kamfani mafi shahara da kirkira,” in ji shi.

Sauye-sauyen na zuwa ne yayin da Mr Bezos ya kara zama sananne a shafukan sada zumunta.

Ya fuskanci takun-saka da masu fafutikar kan nuna daidaito da kare hakkin ma’aikata, kana ya zuba dukiyarsa cikin wasu harkokin kasuwanci kamar na kamfanin ayyukan binciken sararin samaniya ‘Blue Origin’ da kuma jaridar ‘Washington Post’.

‘Ba barin kamfanin zai yi ba’

Amazon ya kuma fuskanci karuwar yawan bincike daga hukumomin sa-ido kan kauwanci, wadanda ke tuhumar karfin ikon mamaye kasuwanni da kamfanin ya yi, da suka hada da na bangaren na’urori masu kwakwalwa da sauran kamfanonin fasahar kere-kere kamar su Microsoft da Alphabet jigo da kamfanonin Google da YouTube ke kalubalantarsa.

Matakin da Mr Bezos ya dauka na mika ragamar ayyukan yau da kullum na kamfanin ya zo da mamaki.

Amma kuma da alamu masu zuba jari ba su nuna damuwa ba, yayin da aka dan samu sauyi a farashin zuba jari a kamfanin bayan wasu sa’o’i na hulɗar cinikayya.

Yayin wani kira ga masu sharhi don tattaunawa kan sakamakon cinikin kamfanin, babban jami’in harkokin kudi na Amazon din Brian Olsavsky ya ce: “Jeff ba wai zai bar kamfanin ba ne, zai kama sabon aiki ne… babban aiki ne mai matukar muhimmanci a cikin jerin a fannin bunkasar ayyukan na Amazon.”

Jeff Bezos

Mr Jassy, ya kammala karatu daga Jami’ar Harvard, kuma tun a shekarar 1997 ya fara aiki da Amazon, kuma ya taimaka wajen kirkiro shafin yanar gizo na ayyukan kamfanin, wanda aka dade ana yi wa kallon wani babban tushen samun ribar kamfanin.

“Andy sananne ne a cikin kamfanin, kuma kamar yadda na dade, haka shima ya dade a kamfanin. Za kasance shugaba nigari, kuma na matukar yarda da aikinsa,” in ji Mr Bezos.

Sophie Lund-Yates, wata mai yin sharhi ce a Hargreaves Lansdown, ta kuma ce ” babu mamaki” cewa Amazon ya zabi shugaban bangaren ayyukansa na na’urori masu kwakwalwa ya jagoranci kamfanin.

2px presentational grey line
Analysis box by James Clayton, North America technology reporter

Wannan babban abin mamaki ne. Amma dole a tuna cewa shi kansa Jeff Bezos na da kimanin kusan dala biliyan dari biyu ($200bn).

Kuma muddin kana da irin wannan arziki, ka tuna abinda za ka iya yi. Jeff Bezos yana da buri da yawa da ya wuce cikin Amazon.

Kamafinsa na Blue Origin na son ”gina hanya zuwa sararin samaniya”. Ya kuma zuba dala biliyan goma ($10bn) cikin ayyukan ‘Earth Fund’, da aka kafa don taimakawa wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Af, yana kuma da kamfanin jaridar Washington Post.

Ta yaya Amazon zai jure? Amma dai, abu mafi muhimmanci, ba wai zai bar kamfanin bane. A matsayinsa na sugaban mai cikakken iko kuma wanda ya kafa kamfanin, har yanzu yana da karfin fada a ji a kamfanin.

Amma kuma, janyewarsa zai iya kasancewa rashin karfin fada a jin.

Wanda zai maye gurbinsa – Andy Jassy – ya dade yana jagorantar katafaren bangaren ayyukan yanar gizo.

Karin girman da ya samu na nuni da yadda yake da tasiri wajen harkokin kasuwancin kamfanin na Amazon.

2px presentational grey line

A bara ne daya babban jami’in, Jeff Wilke, wanda ya jagoranci bangaren hulɗa da masu sayen kaya na kamfanin, ya sanar da yin murabus dinsa.

Ayyukan yanar gizo na Amazon “sun cigaba da bunkasa a [baya-bayan nan], kana sun samu gagarumin ciniki.

Daukacin ciniki a kamfanin ya karu zuwa kashi 44 bisa dari ( 44%) a cikin watanni uku na shekarar zuwa dala biliyan dari da ashirin da biyar ( $125.6bn), sakamakon sabunta dokar kullen korona a wasu sassan duniya.

Ayyukan shafukan yanzr gizo sun shaida karuwar kashi 28 bisa dari (28%) zuwa dala biliyan goma sha biyu da miliyan dari bakwai ($12.7bn).

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Carolina Milanesi, wata mai sharhi a cibiyar Creative Strategies, ta rubuta a shafinta na Twitter cewa “gagarumar” sanarwar ta nuna yadda bangaren ayyukan yanar gizo ke da muhimmanci ga kasuwancin Amazon.

Amma kuma ta kara da cewa ba ta da yakinin cewa Bezos “ba zai daina yin tasiri a kan makomar kamfanin ba”.

Masu sukar lamirin kamfanin suma sun mayar da martini game da sanarwar.

“Kada ku bari Amazon ya yaudare ku. Har yanzu Jeff Bezos yana da karfin fada a ji a matsayinsa na shugaba mai cikakken iko,” in ji kungiyar Public Citizen, kungiya mai rajin kare ‘yancin masu sayen kaya a Amurka.

“Akwai bukatar yin garanbawul game da wannan mulkin mamaya da danne hakki.”on.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku