Connect with us

Manhaja

Manhajar WhatsApp ta kusa daina aiki akan wasu wayoyi

Published

on

Manhajar WhatsAPP

Manhajar WhatsApp ta kusa daina aiki akan wasu wayoyi

Tirkashi!!! Kunji fa. Kamfanin WhatsApp ya sanar da hakanne ga masu amfani da wannan manhaja a bisa dalilai masu karfi, duba da yadda matakan tsaron wasu nau’in wayoyin ke zama barazana ga ita wannan manhaja.

Kamfanin manhajar ya sanar da cewa daga 1 ga watan Janairun shekarar 2020, dukkan wayoyin dake amfani manhajar sarrafawa ta windows (windows phones) amfani da manhajoji mallakin Facebook ya haramta garesu (windows phones). Haka zalika wayoyi samfurin Android masu amfani da tsohuwar manhajar android (Older Version of android) kai har ma da wayoyi samfurin iPhone wadanda ke amfani da tsohuwar manhajar sarrafawa ta iOS suma za a dakatar da basu kulawa ta fuskar tsaro daga karshen watan janairu 2020.

Kamfanin ya kara da cewa haramtawa tsofaffin manhajar sarrafawa(older operating system) ga wasu wayoyi ya zamo tilas domin inganta matakan tsaro ga manhajar WhatsApp. Kasancewa a halin yanzu Kamfanin WhatsApp ba zai iya cigaba da bawa tsofaffin manhajojin kulawa ba, saboda wasu daga cikin sassan sarrafa manhajar whatsapp (Features) ba za suyi aiki akan su ba.

Wayoyi samfurin Android masu amfani da tsohuwar manhajar sarrafawa (Android Version 2.33 ginger bread) da kuma wayoyi samfurin iPhones masu amfani iOS 8 ko kasa da haka dukkan su zasu yi rashin samun damar cigaba da amfani da manhajar WhatsApp.

Kamfanin Apple ya daga darajar manhajar sarrafawa ta iOS zuwa iOS 8 a shekarar 2014. Hakan yana nuna cewa duk wanda ke amfani iPhone 6 ko sama da haka zamu iya cewa sun shallake. Sannan kuma ita manhajar sarrafawa ta iOS za ta iya aiki da samfurin iPhone 4s, iphone 5, iPhone 5c da kuma iPhone 5s, dan haka zai fi kyau masu ire-iren wadannan samfuran wayoyi su tabbata sun daga darajar (update) na’urorin su idan har basu riga sunyi hakan ba tuntuni.

Amma kuma mamayar zata fi yawa ga masu amfani da wayoyisamfurin Android, duba da sune suka fi yawa wajan ta’ammali da manhajar WhatsApp. Samfurin Android GingerBread ya fara aiki ne  a shekarar 2010 hakan ya tabbatar da cewa samfuran wayoyi Googel, Huawei, Samsung da kuma Sony da suka fara aiki shekaru 10 baya, wannan matsalar baza ta shafe su ba. Haka kuma samfuran wayoyin da ka kera su kafin shekarar 2010 suma zasu iya tsallakewa idan sun yi kokarin daga darajojin manhajojin sarrafawar su (sytem update).

A karshe an bada shawara ga masu amfni da windows phones, da suyi hanzarin tattara bayanan firarrakin (chat history) su na whatsapp kafin kurewar lokaci. Ta hanyar ‘Expot Chat’ daga cikin bangaren gudanarwa na manhajar.