Connect with us

Featured

Masu karya dokar hana amfani da shafin Twitter a Najeriya

Published

on

masu karya dokar hana amfani da shafin na sada zumunta

Ƙurar da ta tashi sakamakon dakatarwar da gwamnatin Najeriya ta yi wa shafin sada zumunta na Twitter daga ƙasar tana ci gaba da turnuƙe sassa daban-daban na rayuwar ‘yan ƙasar.

A ranar Juma’a ne gwamnatin ta Najeriya ta dakatar da kamfanin daga aiki a ƙasar kwanaki kadan bayan kamfanin ya goge wani saƙo da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa.

A saƙon shugaban, ya yi gargadi ga masu tayar da hankali a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda suke ƙona ofisoshin hukumar zabe da kasshe ‘yan sanda da makamantasu.

Da yake jawabi lokacin da shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya jagoranci tawagar jami’an hukumar suka kai masa, ya ce masu tayar da hankali da son raba Najeriya ba su san abin da ya faru ba ne lokacin yaƙin basasa yana mai cewa zai yi musu magana da yaren da suka fi sani.

Hakan ya jawo martani daban-daban inda wasu suke ganin bai dace ba shugaban ya yi irin wannan kalami yayin da wasu suke cewa furucin ya yi daidai.

Amma shafin Twitter ya goge sakon yana mai cewa Shugaba Buhari ya karya doka, kuma da alama hakan ya yi matukar ɓata ran gwamnatin Najeriya wadda daga bisani ta dakatar da shafin.

A sanarwar da gwamnatin ta bakin ministan shari’a Abubakar Malami ta fitar, ta umarci daraktan gabatar da kara na tarraya ya yi hanzarin tuhumar hukumomi da jami’an da suka ki bin umarnin gwamnatin kasar na daina amfani da shafin Twitter.

Sanarwar ta umarce shi ya hada gwiwa da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin arzikin intanet ta kasar da hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa da sauran hukumomin da ke da alaka da irin wannan aiki domin ganin hakan ya tabbata.

‘Ƙusoshin Gwamnati masu karya dokar gwamnati’

Sai dai duk da wannan umarni da gwamnatin ta Najeriya ta yi, wasu kusoshin jam’iyyar da ke mulkin kasar ta APC da hukumomi sun karya dokar tata.

Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna da takwaransa na jihar Oyo Seyi Makinde da na jihar Ondo Rotimi Akeredolu da kuma hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta NDCD duk sun wallafa sakonni a shafukansu na Twitter duk da hanin da gwamnati ta yi.

Alal misali, Gwamna Makinde, ya wallafa sakon da ke bayyana kaduwarsa bisa harin da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai a yankin Igangan, Ibarapaland a jihar Oyo, a safiyar Lahadi, lamarin da kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.

Shi ma Gwamna Akeredolu ya wallafa sakon Twitter ranar ta Lahadi inda ya ce sun umarci Kwamandojin rundunar tabbatar da tsaro ta Kudu Maso Yammacin kasar, ta kira taron kwamandojinta domin soma ayyukan tabbatar da tsaro nan take.

A nasa bangaren, Gwamna Nasir El-rufai, ya wallafa wata maƙala da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya buga wanda ke cewa Najeriya ta koya wa Amurka yadda za ta tafiyar da manyan kamfanonin sadarwa.

Ita kuwa hukumar NCDC ta wallafa alkaluman da ta saba fitarwa a shafin Twitter kan mutanen da suka kamu da cutar korona da misalin karfe 12 da minti biyu na safiyar Asabar.

A ranar Litinin din nan ne Hukumar Harkokin Yaɗa Labarai a Najeriya ta National Broadcasting Commission (NBC) ta umarci dukkan kafofin yaɗa labarai da su goge shafinsu na Twitter nan take.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon haramta amfani da dandalin da gwamnatin ƙasar ta yi.

Hukumar ta umarci kafofin labarai da su “goge shafukansu sannan su daina amfani da Twitter a matsayin hanyar samun labarai (UGC) musamman a shirye-shiryen da ake buga waya”.

Sanarwar da Farfesa Armstrong Idachaba ya sanya wa hannu ta ce: “Sashe na 2(1) na dokar NBC ya sharɗanta cewa hukumar na da haƙƙin tlasta bin dokar ƙasa da tsare-tsare.

“Kazalika, sashe na 3.11.2. ya tanadi NBC ta tilasta aiwatar da doka a kowane lokaci a yanayin da aka tabbatar cewa doka da oda sun zarta aikata laifi da kuma hatsaniya.”

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku