Connect with us

Labarai

Masu kutse sun saci bayannan sirrin mutane miliyan ashirin

Published

on

dandalin-manhajoji-na-aptoide

Masu kutse sunyi nasarar sace bayannan sirrin kimanin mutane miliyan ashirin a dandalin manhajojin Android na Aptoide. Kuma su yada bayanan da suka sace a zaurukan su na ‘Yan ta’addan Intanet (Hacker Forum).

Masu amfani da waya samfurin Android suna da ikon shiga da sauke manhajoji kimanini miliyan uku (3 million) daga babban shagon manhajojin Android (Google Play Store). Sannan bayan Google Play Store, akwai sahihan shafukan manhajojin android kamar Samsung galaxy store da kuma Huawei App Gallery wadanda kamfanoni sahihai suka samar da su.

Bugu da kari, kuma akwai wasu shafuka, matattarar manhajojin android masu zaman kansu wadanda akewa lakabi da ‘third-party apps store’ (Amazon App Store, ApkPure, F-Droid, APKUpdater, QooApp, Yalp Store, XDA Developers, Blackmart Alpha, ACMarket da sauran su..) kuma manhajar su bata zuwa akan wayar android (preinstalled), kuma ba’a samun ireiren manhajojin su a Google play store. Daga cikin su Aptoide shi ne mafi girma wajan shahara. Kasancewar yanada dumbin jama’a kimanin miliyan dari da hamsin (150 million) dake mu’amala da manhajojin su, wannan dandali yana da kimanin manhajoji miliyan daya (1 million).

Dan ta’addan ya samu nasarar awon gaba da muhimman bayanan sirri na kimanin mutane miliyan talatin da tara (39 million) dake mu’amala da manhajojin shafin na Aptoid sannan ya yada bayanai (username, emails da passwords) na mutane miliyan ashirin ga shahararrun zaurukan ‘yan ta’addan intanet (popular hacker forum).

Kusan a lokuta da dama masana harkokin tsaro na intanet sukan yi gargadi ga jama’a da su guji aiki ko mu’amala da manhajojin rukunin third-party. Saboda tsaro.

Bisa tsari irin na fasaha, jama’a masana harkokin samar da manhajoji (App developers) sukan mallaki gurabe a play store domin dora manhajojin da suka kera da nufin siyarwa ko kuma kyauta ga masu amfani da wayoyi samfurin android. Hakan yasa kowa yanada ikon killace gurbinsa da username da password masu tsauri domin kaucewa sharrin masu kutse. Sai kuma katsam gashi ya faru da Aptoid Users.

Wannan kamfani ko shafi na Aptoidi an samar da shi a shekarar 2011. Wanda cikin kankanin lokaci ya samu kar buwa a wajan masu sarrafa wayoyin Android. Wanda a farkon lokaci shugaban kamfanin yayi ikirari akan karfin matakan tsaro da suke da shi. Dukkanin manhajojin dake shafin nasu an tantance su, an tabbatar babu gurbatattun manhajoji ko cutar virus. Bugu da kari suna da wata shimfida ta musamman domin tsaurara matakan tsaro.

Continue Reading