Connect with us

Fasaha

Matakan Tsaro na VPN da Proxy a Intanet

Published

on

Matakan Tsaro na VPN da Proxy server

Matakan Tsaro na VPN da Proxy a Intanet.

Wadannan kalmomi guda biyu hanyoyi ne ko ince matakan tsaro ne da ake amfani da su a kafar sadarwa ta intanet, domin toshe duk wata baraka da zata bada damar satar bayanai, kutse da sauran ta’addanci da ke faruwa a Intanet.

Proxy ya kasance tsari ko manhaja da ake amfani da shi domin tabbatar da tsaro, karin sauri wajan isarwa da karbar sakonni, killacewa da kuma kasancewa mahada tsakanin na’urori guda biyu (Client da Server) yayin mu’amala a intanet.

A duk lokacin da za a ziyarci shafin intanet, ana rubuta adreshin shafin a inda aka tanada (address bar), sannan ita na’urar Kwamfuta ko Waya (client) zata aika sakon kai tsaye zuwa ga babban rumbun shafukan intanet (Web Server) da ke dauke da shafin da ake so a ziyarta. Cikin nasara shafin zai bude a kan Kwamfuta ko wayar. A wannan alaaka ta kaitsaye babu cikakken tsaro kamar yadda ake bukata.

Misalin-proxy-server

Misalin Sadarwa ta hanyar amfani da matakin tsaro na Proxy

Amma idan akayi amfani da proxy sakon (request) baya tafiya kai tsaye zuwa ga Babban rumbun Shafukana Intanet (Web Server). Sakon zai isa ga Kwamfuta proxy. Daga nan tsarin proxy zai isar da sakon zuwa ga babban rumbun shafuka (web server), ba tare da ya bayyana sirrin na’urar da akayi amfani da ita ba a matakin farko. Wannan kadan kenan daga cikin aikin proxy na boye sirri. Proxy yana boye siri akan kasar da mutum yake, lambobin siri na sadarwa suma yakan boye su da sauran muhimman bayanai. Proxy yana amfani a matakin manhajar watayawa a intanet (Web Browser) wadda da ita ake bincike a intanet. sannan baya ba da tsaro ga sauran manhajojin dake kan na’ura.

Manyan kamfanoni, ma’aikatun gwamnati da Bankuna suna amfani da proxy domin su boye, su killace dukkan mu’amalar sadarwa a kowanne lokaci. Kuma Tana basu kariya musamman ga masu kutse da sauran matsalilin hanyoyin sadarwa na intanet. Domin amfani da wannan tsari na proxy akwai (1) na Kudi wato Premium Proxy da kuma (2) na Kyauta wato Free Proxy. Sannan kuma akwai manhajoji da za’ayi amfani da su domin amfani dasu akan na’urorin Kwamfuta da Wayar Zamani.

VPN (Virtual Private Netwrok) shi ma kamar proxy ana amfani da shi domin kara karfin tsaro da killace alaakar sadarwa tsakanin na’urori da intanet. Kusan VPN yafi bada cikakken tsaro fiye da proxy amma dukkanin su san kasancewa a tsakanin na’urori guda biyu, Kwamfuta ko Waya da kuma Intanet.

Matakin tsaro na VPN yana aiki ne a matakin manhajar sarrafa na’ura (Operating System), ta yadda dukkanin manhajojin dake kan na’ura za su amfana da matakan tsaro na VPN. Sannan VPN yana boye lambobin sadarwa (IP Address) ta yadda duk mu’amalar da akayi a intanet ko shafin da aka ziyarta ba za su gane daga inda mutum yake ba (Location). VPN yakan rage saurin intanet kasancewar yana da sarkakiya a cikinsa domin bada cikkaken tsaro ga hanyar sadarwa tsakanin na’ura da intanet.

misalin-vpn-server

Misalin Sadarwa ta hanyar amfani da matakin tsaro na VPN

Duba da yadda bukatar amfani da intanet ya kara yawaita a Duniya, musamman a wannan lokaci da annobar coronavirus ta mamayi kasashen duniya masu yawa, har ta haddasa rufe makarantu, ma’aikatu, kasuwanni, masallatai, coci-coci da sauarn tarurruka, domin dakile yaduwarta ga jama’a.

Rufe makarantu, Kasuwanni, da Ma’aikatu domin dakile yaduwar wannan cutar a tsakanin al’aumma, baya nufin an daina karatu, kasuwanci da aiyuka a’a. Ana amfani da fasaha wajan gudanar da dukkan al’amuran kamar yadda aka saba.

Tuntuni akwai tsare-tsare da fasaha ta samar wanda ake iya gudanar da komai daga gida koma ince daga cikin daki, ta hanyar amfani da tsarin sadarwa na intanet. Misalan hanyoyin mu’amala daga gida ta hanyar intanet; Teleconfrencing, Video calls, Video Conferencing da sauran hanyoyi hadi da manhajoji da ake iya tattaunawa kaitsaye har ma da ganin juna yayin tattaunawa.

Saboda haka matakan tsaron dana bayyana a sama sune ake ta amfani dasu domin killacewa da tsaurara tsaro a dukkan sadarwa tsakanin ma’aikata da matattarar bayanan kamfanonin (database server) da suke aiki, da kuma tasakanin Dalibai da matattarar bayanan makaranta da dakunan karatun zamani. Haka suma ‘Yan Kasuwa.

Da fatan Allah ya Kare mu, ya bawa wadanda suke fama da wannan annoba lafiya. Allah ya amfanar damu.