Connect with us

Intanet

Me ake nufi da Intanet?

Published

on

Intanet

Yanada matukar muhimmanci a wannan lokaci a samu kyakkyawar fahimtar kalmar Intanet. Duba da yadda ta zamo jigo a rayuwar mu ta yau da kullum a kowanne fanni na aiki. Haka zalika akwai bukatar a fahimci kalmar Network domin a samu ingantacciyar fahimta akansu gaba daya.

Kalmar Network tana nufin alakar sadarwa (link) daga Na’ura zuwa wata na’ura ko kuma daga kwamfuta zuwa wata kwamfuta.

Haka itama kalmar intanet tana bayyana alakar sadarwa tsakanin na’urori na duniya baki daya. Dan haka akwai matakai na kulla alakar sadarwa a tsakanin na’urori (Kwamfuta da dange-dangen ta) domin a sami damar yin musayar aiyuka ba tareda anyi mu’amala ta zahiri ba.

Alakar sadarwa ta intanet itace kanwa uwar gami wajan isar da sakonni cikin sauri kamar kiftawar ido. A cikin ta ne aka samu damar yin mu’amala tsakanin jama’a dake kasashe daban-daban ba tare da anyi mu’amala ba ta zahirance.

Hasali ma ta dalilin intanet ne duniya ta zamo tamkar a tafin hannu. Ana gudanar da al’amura masu yawan gaske a rayuwar mu ta yau da kullum, kama daga;

  • Kasuwanci
  • Sada zumunci
  • Aikawa da karbar sakonni
  • Karatu
  • Bincike
  • da sauransu…

Kuma wannan alakar sadarwa ta intanet bawai ta tsaya ne a tsakanin kwamfutoci da wayoyi ba kawai, ta hada har da su Jiragen sama da sauran na’urorin dake wataywa a sararin subhana. Jirgin sama yana tafiya ne akan tsarin amfani da alakar sadarwa (NETWORK).

Ana kulla wannan alaka ta hanyoyi kamar haka; (1) amfani da waya domin kulla alakar sadarwa tsakanin na’urori (Wired Network), (2) amfani da fasaha mara waya domin hada na’urori (Wireless).

Akwai tsare-tsare da ka’idojin (Internet Protocol) da sai an bisu kafin a cimma nanufar alakar sadarwa a tsakanin kamar. Lambobi ne ma banbanta da suke bawa na’ura damar kasancewa a kantsarin network.

Cigaban karatu….