Connect with us

Darasi

Me ake nufi da Kwamfuta?

Published

on

Kwamfuta

 

Yanada kyau na fara da bayani akan ma’anar kalmar Kwamfuta. Amma zan tsallake dukkan tarihi, na tafi kaitsaye acikin wannan darasi na farko.

Idan muka kalli tsarin turanci yadda wannan ilimi yazo gare mu, kalmar Computer idan muka dan gutsure wani harafi musamman na karshe (r) ta zama Compute. Kuma tana nufin abubuwa kamar haka; Warware matsala musamman ta lissafi, bayyana gaskiya ko karyar al’amari, ko kuma kaitsaye na ce lissafi. Saboda haka na’urar Kwamfuta tana nufin hnayar warware dukkan matsaloli ta fuskoki daban-daban.

Sannan kuma a tsarin yadda aka samar da ita da kuma yadda take gudanar da aiyuka kamar yadda muke gani a kullum, zan iya bayyanata kamar haka; Kwamfuta ta kasance na’ura daga cikin na’urorin lantarki, wadda ke da ikon karbar kayan aiki (Data) sannan ta sarrafa su (Process)  daga karshe ta bada sakamako (Output) duk a cikin matsanancin sauri. Kamar yadda hoton dake kasa da wannan bayani ya nuna.

Darasin Kwamfuta

Yanada kyau ana gane cewa duk da kirarin da ake yiwa Kwamfuta cewa Na’ura Mai Kwakwalwa, bata da ikon samar da komai da kanta ko yin wani abu na kashin kanta face sai dan Adam ya saka mata dukkan abubuwan da suka kamata kafin tayi duk abinda ta keyi. Kamar yadda aka gani a hoton dake sama Input –> Process –> Output, wadannan kalmomi guda uku suna bayyana aikin kwamfuta gabadayansa. Duk na’urar kwamfutar data amsa sunanta hakika sune tsarin da ta ke bi wajan gudanar da aikin da akeyi da ita.

  1. A matakin farko (input) za a shigar mata da bayanai na irin aikin da ake so ayi da ita tare da umarnin (instructions) yadda akeso tayi aikin. Daga cikin abubuwanda ake shigarwa a wannan mataki (input-data) zai iya zama zallan rubutu (text) domin rubuta labari ko littafi, hotuna, sauti, da faifan bidiyo domin sarrafa su zuwa yadda ake so su kasance.
  2. Mataki na biyu (Process) shine bigiren da ake jerantawa da kuma tsara yadda sakamako zai kasnace daidai da yadda ake so ya kasance. Ya bada cikakkiyar ma’ana yadda za’a fahimci sakonnin dake ciki.
  3. Matakin karshe (Output) anan ne ake samun sakamakon aikin da aka shigar domin sarrafawa.

Haka kuma na’urar Kwamfuta tana da wasu kebantattun al’amura har ma da siffofi (characteristics) wadanda suka kebantar da ita daga cikin jerin na’urorin lantarki har tayi fice ta kuma yi kane-kane a kowanne gurbi na rayuwar mu da aiyukan mu na yau da kullum. Ga su kamar haka:

Speed: Saurin sarrafa aiki
Accurate: Samar da kyakkyawan sakamakon da babu kuskure a cikin sa.
Deligence: Aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba ko Ince Juriya
Large storage: Babban Rumbun adana aiyuka
Versatility: Shiga kowanne bigire ko yin aiki a kowanne fannonin aikace-aikacen yau da kullum.
Reliability: abar dogaro wajan gudanar da aiyuka a kowanne lokaci.
da sauran su…

Na’uarar Kwamfuta tanada Jigajigan sassan kwamfuta guda biyu wadanda kowanne daga cikin su ya dogara da dayan. Wadannan abubuwa sune Hardware da Software.

Mu hadu a darasi na biyu domin cigaban karatu.

Continue Reading