Connect with us

Darasi

Me ake nufi da Shafin Intanet

Published

on

shafukan -intanet

Shafin Intanet

Kamar yadda kowa ya sani Intanet ta zamo wani babban al’amari a cikin harkokin mu na yau da kullum. Saboda zai yi wahala ace gari ya waye har zuwa faduwar rana batare da anyi ta’ammali da intanet ba. Akan duba labarai domin ji ko ganin abinda duniya take ciki, sada zumunta, Harkokin kasuwanci, Neman Ilimi, Binciken tsofaffi da sababbin al’amura da sauransu…

Kamar yadda wannan shafi yayi bayani akan alakar sadarwa ta intanet a baya (wadda ake kullawa  tsakanin na’urori na duniya baki daya), haka kuma a yanzu zamu tattauna akan yadda al’amura suke faruwa a shafukan intanet.

Shafin Intanet hanya ce da akebi wajan dabbakawa ko wallafa (publish) rububce-rubuce kama daga labarai zuwa aikawa da karbar sakonni (email) da sauran aiyuka ma bambamta masu yawan gaske.

Dukkanin rubuce-rubuce cakude da hotuna, murya ko sauti har ma da fayafayen bidiyo da ake sakawa a yanargizo, suna kunshe ne a cikin shafukan intanet domin kowa ya amafana dasu daga sassa daban-daban na duniya.

Ana tsara shafukan intanet ne daidai da abubuwanda za’a wallafa a cikinsa, kuma akan so ya kasance kowa zai iya samun damar shiga domin yin bincike ko karanta abinda aka rubuta a ciki. Akwai wadanda suke akillace (Premium content) ta yadda bakowa ne zai shiga ba domin duba rubuce-rubuce ko al’amuran dake ciki har sai anyi rijista (Subscribe).

Bugu da kari a halin yanzu ana so duk shafin da aka wallafashi a intanet ya kasance za’a iya watayawa ko yin bincike a cikinsa da kowacce irin na’ura, domin bawa jama’a damar dubawa a kowanne lokaci a kowanne yanayi da mutum yake. Ta yadda idan mutum yana gida ko ofis zai iya amfani da Kwamfutar girke (Desktop) ko laptop. haka kuma idan mutum  a tafe yake zai iya amfani da wayar hannu (Mobile) domin bincike a shafin intanet. A takaice ana so shafin ya kasance mai rikida (responsive) domin bawa maziyarcin shafin intanet (site visitor) damar ganin komai a cikin shafin. Kamar yadda hoton dake kasa ya nuna;

shafukan -intanet

Tsarin wallafa shafin Intanet:

Akwai Shafin Farko (Hompage), wanda shine na farko da maziyarci ke fara gani a lokacin zaiyara. Da kuma sauran shafuka wadanda ke kunshe da bayanai game da shafin ko mawallafin shafin (about page), bayanai akan aiyukan shafin (Services), rumbun hotuna (Picture Gallery) shafin tuntuba da adreshi (Contacts Page) da sauransu…

shafukan -intanet

Bayani akan adreshin shafin Intanet; za a gane bamabamce-bambamce a cikin adreshin kamar yadda ake tsarashi. Kuma kowanne yana da ma’ana daya kamata a fahimta.

  • https://duniyarfasahaonline.com
  • https://duniyarfasahaonline.com
  • www.duniyarfasahaonline.com

Na farko daga cikin jerin misalan dake sama (http://), yana nuna cewa shafin bashi da cikakken tsaro kuma baza a iya gudanar da harkokin kasuwanci ko musayar bayanan sirri aciknsa ba.

Na biyu daga ciki misalan (https://) yanada tsaro (secured connection) kuma za’a iya gudanar da dukkan al’amuran da suka dace batare da fargaba ko barazanar rashin tsaro a cikinsa ba.

Na uku yana dauke da karin harafin W har guda 3 kafin adreshin. Yanada kyau a fahimci cewa www ba dole ne ayi amfani dasu ba, domin ko da su ko babu su shafin zai bude indai yana aiki. Kuma harufan  sukan fito da kansu a lokacin da shafin yake budewa. Sannan ko a lokacin yin rijistar adreshin ba’a saka www.

Cigaban karatu… Darasi na 2: Shafukan intanet guda 11 da suka fi shahara

Continue Reading