31 C
Kano
Thursday, October 22, 2020

Microsoft ya bankado yunkurin yin katsalandan a zaben Amurka

Mafi Shahara

Kamfanin Microsoft ya yi gargadin cewa kasashen Rasha, da Iran da kuma China sun soma kaddamar da shirin kutsensu, a kokarin fakon ‘yan siyasa da kungiyoyin da ke da alaka da zaben kasar Amurka na watan Nuwamba.

Kamfanin ya ce ya bankado dukkanin yunkurin da aka yi na satar bayanai, sannan ya dakile dukkanininsu.

Akalla kungiyoyi 200 da ke aiki ga ‘yan takara biyu na zaben shugaban kasar wato Trump da Joe Biden aka so yi wa kutsen.

Masu kutsen wata kungiya mai suna Phosphorus da ke da alaka da rundunar sojin Rasha, da hukumomin Iran sun so satar bayanai daga kwamitin yakin neman zaben shugaba Donald Trump a cewar Microsoft.

Yayin da su kuma masu satar bayanan kungiyar Zirconium da ke da alaka da China suka yi yunkurin kutsawa rumbun adana bayanan kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Democrat Joe Biden, sai dai dukkaninsu, hakansu bai cimma ruwa ba.

Manyan shugabannin jam’iyyar Democrat na zargin wasu manyan ƙasashen waje da kokarin yin katsalandan a zaben watan Nuwamba da ke tafe.

Shugabar majalisar wakilian Amurka Nancy Pelosi da kuma jagoran ‘ƴan Democrats Chuck Schumer a majalisar dattiajai, sun bayyana damuwa cewa ana kokarin amfani da majalisa domin yada labaran karya.

A cikin wata wasika da suka aikawa hukumar FBI, shugabanin Democrats ɗin sun bayyana damuwa kan barazanar da suka ce ke tattare da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Sun ce barazanar ta kunshi wani yunkuri na ƙaddamar da wani kamfen na kokarin yada wata farfagandar karya.

Tushen Labari

Karin Wasu

Sababbin Wallafa