Connect with us

Shafukan Zumunta

Muhimmancin Shafin Zumunta na LinkedIn

Published

on

shafin zumunta na linked in

Muhimmancin Shafin Zumunta na LinkedIn.

LinkedIn ya kasance daya daga shafukan zumunta da ake amfani da su a rayuwar yau da kullum. Wannan shafi na linkedin ya bambanta da sauran shafukan zumunta, dandali ne da tara kwararru na fannoni daban-daban daga sassan Duniya. An samar da shi a kasar amurka a 28 ga watan disamba shekara ta 2002, kuma an kaddamar da shi a 5 ga watan Mayu, 2003.

Shafi LinkedIn, ana amfani da shi a matsayin matattara ko dandalin kwararru, wanda har akan bayyana mataki da matsayin karatu da sauran bayanai domin samun aiki kamar yadda manyan kamfanoni da ma’aikatu suke amfani da shi wajan daukar ma’aikata.

‘Yan Kasuwa musamman wadan da suke gudanar da harkokin akan tsari irin na zamani suna amfani da shi wajan habbaka kasuwanci da fadada lakar kasuwanci a duniya baki daya. Wannan shafi yana bada damar kullawa da kara bunkasa mu’amala a tsakanin masana da kwararru na kowanne fannin ilimi daga sassan duniya baki daya, fiye da yadda ake amfani da sauran shafukan zumunta kamar su; Facebook da Twitter.

LinkedIn ya zamo dandalin tallata matakin ilimi, Basira, Fasaha, Hazaka da sauran su… Ana tarayya domin karin fahimta tsakanin jama’a musamman akan abubuwan cigaba ta fannoni daban daban. Kwararre yakan iya bada sheda akan daya daga cikin abokan mu’amala a shafin linkedin  musamman akan kwarewar aiki ko sana’a.

Duba da yadda bukatar samun aiyukan yi ya zama a duniya baki daya, wannan shafi na linkedin ya zamo waraka ga kowa. Kama Manyan kamfanoni masu zaman kansu da ma na Gwamnati sukan baza komar neman kwararru a fannoni masu yawa, haka zalika duk wanda ka gani a wannan shafi yasan abinda yakeyi kuma zai iya tabbatar da duk abubuwan da ya rubuta a bangaresa ta fuskar ilimi, kwarewa ko sana’ar da ya iya. babu karya babu coge.

Kuma a wannan shafi mutum yanada zabi akan mutanen da zai kulla alaaka da su, tun daga abokan aiki na zahiri, tsofaffin abonkan aiki, har ma da sababbin fuskoki da akayi tarayya wajan ilimi, fikira, fasaha, kasuwanci har ma da kwarewa akan wasu al’amura masu matukar muhimmanci a rayuwa. Kowa yanada ikon duba bayanan kowa (profiles) domin fahimtar gwagwarmayar sa ko matsayin sa.

A wannan dandali na linkedin ana iya wallafa maqaloli akan abubuwa daban daban domin ilimantarwa, fadakarwa harma da nishadantarwa. Akan wallafa labaran duniya. Manyan kamfanoni suna wallafa bayanai akan kayayyakin da suke kerawa, bayanai akan sababbin al’amura, tattaunawa da abokan huldar kasuwanci domin ingantawa da bunkasawa.

Kuma kowa zai iya tallatawa ko sanar da abokan mu’amalar sa abubuwa kamar su; Litattafai, shafukan intanet da sauran su.. duk a shafin na linkedin. Sannan kuma a shafin Linkedin ana kiran abokan mu’amala da Connections, sabanin yadda sauran shafukan zumunta suke abokai ko mabiya (Friends or Followers). Kuma alaakar kusa tafi ta nesa. Saboda haka wanda yake nesa da kai a matkin alaaka baza ka iya aika masa da sakon sirri ba. Misalin kamar abokin, abokin abokin ka.

A karshe nake kara jaddada muhimmancin Shafin LinkedIn, musamman ta fuskar nema da samun aiyukan yi ga kwararru ko wadanda sukayi shuhura a wasu sana’o’i. Kuma akwai ‘yar jarrabawa da akanyi a bangarorin ilimi wanda mutum yanada zabi wajan yin su, haka kuma sakamakon su yana bayyana a shafin mutum domin kara masa armashi wajan samun aiki ta wannan shafi. dan haka wannan babbar dama ce ga kowa, ya mallaki gurbi a Shafin Linkedin. Baya ga shafin intanet, linkedIn suna da manhaja (Mobile Apps) da ake amfani da ita akan wayiyin zamani.