Connect with us

Featured

Najeriya ta bi sahun kasashe wajan tsaurara dokoki akan aiyukan internet

Published

on

muhammadu buhari 1

Shafin Twitter ya amince da wasu jerin sharuda domin kawo karshen dakatar da shi a Najeriya, wanda ake ganin hakan wata babbar nasara ce ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kokarinta na takaita abubuwan da ake yi da intanet, in ji wasu masana.

Yanzu dai Najeriya ta bi sahun kasashe irin su India da Indonesia da kuma Turkiyya, wadanda suka tsaurara dokoki a kan ayyukan kamfanonin intanet. Wannan wani abu ne da wasu kasashen Afirka za su iya kwaikwayo wajen hana ‘yan hamayya amfani da shafukan sada zumunta da muhawara wajen janyo kungiyoyin da ba sa jituwa da gwamnati.

Wasu daga cikin dokokin da Twitter ya amince da su sun sanya tunani da fargaba a kan yadda ayyukan shafin za su iya kasancewa a nan gaba a kasar.

“Lalle abin damuwa ne ganin yadda Twitter ya amince da yarjejeniyar da za ta iya sa shi daukar matakin da Najeriya za ta iya matsa masa ya dauka a nan gaba, in ji David Greene, daraktan wata kungiya mai zaman kanta a Amurka, Electronic Frontier Foundation (EFF), a tattaunawarsa da Manema Labarai.

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku