Connect with us

Featured

Najeriya ta sanya SharaɗI kafin a buɗe shafin Twitter

Published

on

najeriya ta sanya sharaɗi kafin a buɗe shafin twitter

Gwamnatin Najeriya ta gindaya sharadin da sai an cika shi za ta janye dakatarwar da ta yi wa shafin Twitter a kasar.

Ministan harkokin kasashen wajen kasar ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da wasu jakadun kasashen waje ciki har da na Burtaniya da kuma Amurka a ranar Litinin a Abuja.

Wannan dai na zuwa ne bayan da jakadun suka soki matakin na Najeriya na dakatar da Tuwita a makon jiya, lamarin da kuma har yanzu ke ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce.

Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya ta gana da jakadun Burtaniya da Canada da Amurka da kuma Tarayyar Turai ne.

Ministan ma’aikatar Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa ganawar na da kyau don su yi musayar ra’ayoyi da jakadun cikin mutuntawa.

Mista Onyeama ya ce saboda kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu da kasashen ya sa suka dauki tsokacin da suka yi game da dakatar da Twitter a Najeriya da mahimmanci, kuma wannan dalili ne ya sa suka gayyace su don tattaunawa da kuma fayyace wasu abubuwa.

Ministan ya kara da cewa za su mayar da aikace-aikacen Tuwita a Najeriya idan ya kasance za a yi amfani da dandalin yadda ya kamata.

“Ba mu ce Twitter na yi wa ƙasarmu barazana ko wani abu ba, dalilin da ya sa muka dauki wannan matakin shi ne don dakatar da dandalin daga yin amfani da shi wajen wargaza al’umma da taimaka wa wajen aikata miyagun laifuka.”

Mista Onyeama ya nanata cewa Najeriya ba za ta zuba ido kafafen sada zumunta su rura wutar rikici da raba kawunan ‘yan kasar ba.

Amma da aka tambaye shi ko yaushe za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Twitter sai ya ce a yanzu ba a sanya rana ba.

Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard, ita ce ta yi magana a madadin jakadun Burtaniya da Kanada da Ireland da kuma Tarayyar Turai a yayin zaman tattaunawar.

Ta kuma tunatar da hukumomin Najeriya cewa kafafen sada zumunta na da mahimmanci inda ta nuna farin ciki da cewa kasar na tattaunawa da kamfanin Twitter don samun mafita.

“Mun zo nan ne a matsayin manyan ƙawayen Najeriya da muke cike da fatan ganin ta yi nasara tare da samun hadin kai da zaman lafiya tsakanin ‘yan kasar da kuma karuwar arziki.

“Wadannan su ne manyan abubuwan da muka fi mayar da hankali a kai.

“Duk da cewa akwai tarin kalubale a gaban kasar amma za a iya shawo kansu da hadin gwiwar wadannan jakadu ba kawai ta fuskar tsaro ba, har ma da daukaka zaman lafiya da wanzar da sulhu, wannan abu ne mai muhimmanci.”

A karshen mako ne dai cikin wata sanarwar haɗin gwiwa jami’an diflomasiyyar kasashen suka soki dakatarwar da hukumomin Najeriya su ka yi wa Twitter a kasar, inda suka ce ‘yancin fadin albarkacin baki wani ɓangare ne na ci gaban dimokuradiyya.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku