Connect with us

Kimiyya

Nasa ta shelanta zuwa duniyar Venus wadda ke kusa da Rana

Published

on

nasa ta shelanta zuwa duniyar venus wadda ke kusa da rana

Nasa ta sanar da shirinta na aika masu bincike har tawaga biyu zuwa duniyar Venus domin su binciko yadda yanayin sararin samaniyar duniyar yake da kuma kasarta.

Aikin, wanda a yanzu aka ware masa kudi har dala miliyan 500, za a ƙaddamar da shi tsakanin shekarar 2028 da kuma 2030.

Wani jami’i a Nasa Bill Nelson ya ce aikin zai bayar da dama “a gano wasu abubuwa a duniyar da rabonmu da zuwa can sama da shekara 30 kenan”.

Bincike na karshe da Amurka ta yi kan duniyae shi ne na Magellan orbiter a shekarar 1990.

Sai dai sauran jiragen da ke zuwa samaniya daga Turai da Japan sun ci gaba da zuwa tun daga sannan.

Ayyukan zuwa samaniya sun yi ta kunno kai biyo bayan wasu biyu da aka yi, daga nan kuma ake zaɓa la’akari da darajar ayyukan ta fuskar kimiyya da kuma bunkasar shirinsu.

An zaɓi tura tawagar ne bayan da aka sake nazari sai aka zaɓi zuwa duba da abubuwan kimiyyar da ke can.

Bill Nelson speaks at Nasa HQ in Washington, DcC 2 June 2021

Shugaban Nasa Bill Nelson ya sanar da zuwa Vebus din ne a ranar Laraba 2 ga Yunin 2021 – Asalin hoton, Reuters

“Wadannan tagwayen ayyuka za su mayar da hankali ne kan fahimtar me ya sa duniyar Venus ta zama kamar wata duniyar wuta, da take iya narka duk wani abu da ke cikinta,” in ji Mista Nelson.

Venus ita ce duniya ta biyu da ke kusa da rana, duniya ce da ta fi kowacce zafi inda take da yanayin zafi da ya kai salshiyos 500 – zafin da zai iya narka komai da ke cikinta.

Shirin Davinci shi ne na farko (Deep Atmosphere Venus Investigation of Noble gases, Chemistry, and Imaging) wani aiki ne da zai yi nazari kan zafin duniyar tare da gano yadda ta samu da yadda abubuwa ke kasancewa a cikinta. Kuma zai mayar da hankali kan ko an taɓa samun ruwa a Venus.

Shirin Davinci ana sa ran zai dawo da hoto na farko na duniyar kan yadda filin cikinta yake. Masana kimiyya sun yi amannar za a iya kwatanta nahiyar da suka yadda duniyarmu take, ko ita ma Vnus na kan zirin layin da ya zagaya duniyar.

Sai shirin Veritas (Venus Emissivity, Radio Science, InSAR, Topography, and Spectroscopy), wanda shi ne na biyu, zai yi nazari kan taswirar saman duniyar domin fahimatar tarihin yanayinta da kuma bincikar yadda ta zama daban da duniyarmu ta Earth.

Za a yi amfani da na’urar da ke hango jirgi domin gano saman duniyar don ganin ko ana yin aman wuta da girgizar ƙasa a yankin.

“Abu ne mai ban mamaki ganin ba mu san abubuwa da yawa ba kan Venus, amma idan muka hada duka sakamakon wadannan ayyukan za su fada mana mece ce duniyar tun daga yadda gajimaren saman yake, zuwa aman wutar da ake yi har zuwa kananan abubuwan cikinta,” in ji Tom Wagner wani masanin kimiyya da ke aiki da Nasa.

“Zai zama kamar sai yanzu muka gano duniyar,” ya ƙara da cewa.

Yadda Duniyar Venus take

Sama da shekara 20 duniyar Mars ta mamaye kasafin kudaden da Nasa ke warewa na zuwa sauran duniyoyi. A gefe guda kuma, masu bincike kan Venus sun damu kan yadda ba a bai wa duniyar muhimmanci.

Amma hakan ya fara sauyawa. Sabbin tunani, fahimta da kuma yadda sabbin mutane ke buɗa fahimtarsu kan maƙwabciyar duniyar tamu. Wasu na tunanin akwai yanayi da mutane za su iya nazari a kai, da yiwuwar ana samun aman wuta lokaci zuwa lokaci.

Wataƙila an taɓa samun tekuna a biliyoyin shekaru baya a tarihi.

Masana kimiyya da suka sadaukar da ƙwarewarsu don fahimtar wannan duniya na cike da farin cikin cewa a ƙarshe batun bincike a Venus ya dawo teburin Nasa.

Venus volcano

Bayanan hoto, Artwork: Mai yiwuwa a yau wasu duwatsu na aman wuta a Venus – Asalin hoton, NASA

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku