Connect with us

Kimiyya

NASA tayi nasarar aika jirgi marar matuƙi na farko zuwa duniyar Mars

Published

on

jirgi mai saukar ungulu kuma marar matuki a duniyar mars
nasa tayi nasarar aika jirgi marar matuki zuwa duniyar mars

NASA tayi nasarar aika jirgi marar matuki na farko zuwa duniyar Mars – NASA

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta ce ta yi nasarar aika wani karamin jirgi marar matuƙi zuwa duniyar Mars, jirgin ya kasance na farko da aka tura.

Hotunan tauraron ɗan adam daga duniyar ta Mars sun tabbatar da wannan nasarar.

An yi ta shewa da tafi a ɗakin sarrafa na’urorin tauraron ɗan Adam yayin da aka haska hotunan jirgin, waɗanda mutum-mutumin nan da NASA ta aika duniyar ta Mars ya ɗauka.

Jirgin mai saukar ungulu mai suna Ingenuity ya tashi a cikin iskar Mars, ya yi shawagi sannan ya sauka bayan daƙiƙa arba’in.

Ana sa rai wannan fasahar za ta sauya ayyukan sararin samaniya nan gaba, inda za ta ba da damar yin bincike a duniyoyin da ba za a iya tura mutum-mutumi ba.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku