Connect with us

Labari

Ofisoshin Kamfanonin Sadarwa dake Kasashen Afrika

Published

on

ofisoshin kamfanonin sadarwa dake kasashen afrika getty images

Har yanzu ana ci gaba da yin muhawara a shafin Twitter bayan da kamfanin ya sanar da cewa zai bude ofishinsa a kasar Ghana.

Twitter ya ce ya bude ofishinsa a kasar ne saboda tana bayar da damar fadin albarkacin baki sannan za ta kasance kasa da zai ji dadin yin kasuwanci.

Mutane da dama suna bayyana ra’ayinsu kan yadda manyan kamfanonin sadarwar na Silicone Valley suke bude ofisoshinsu a Afirka.

Ya zuwa yanzu, Najeriya ta kasance kasar da kamfanoni uku na sadarwa suka bude ofisoshinsu kana ta taba karbar bakuncin mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg da takwaransa na Twitter Jack Dorsey.

Najeriya

A watan Satumbar 2020 ne Facebook ya ce zai bude ofishinsa a Lagos wanda zai soma aiki a tsakiyar 2021.

Microsoft ya bude wani ofishi a Lagos a watan Yulin 2020.

Google ya biyo baya inda ya bude ofishi a Lagos a watan Janairun 2020.

Ghana

Google ya bude ofishinsa na kan da ke bincike kan fasahar Artificial Intelligence a birnin Accra na Ghana a 2018.

Buhari da Mark Zuckerberg

Bayanan hoto: Zuckerberg ya je Najeriya a 2016 – Asalin hoton, AFP

Afirka ta Kudu

Facebook ya bude hedikwatarsa ta farko a Afirka a birnin Johannesburg a watan Yunin 2015.

A watan Maris, Google ya bude ofishinsa na farko a Cape Town da Johannesburg.

Kazalika a watan Afrilu Amazon ya bude ofishinsa a Cape Town.

Amazon yana da ofis a Cape Town tun 2004.

Kenya

Microsoft ya bude cibiyarsa ta farko a Afirka a Nairobi, babban birnin Kenya a watan Mayun 2019.

A watan Yulin 2020, Microsoft ya sanar da kaddamar da Cibiyar Bincike ta Afirka.

Tushen Labari

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku