Connect with us

Featured

Ruɓaɓɓun motoci ake sayar wa ‘yan Afrika

Published

on

Ruɓaɓɓun motoci ake sayar wa 'yan Afrika

Manyan kasashe masu arziki na duniya na yasar da motoci masu fitar da gurbataccen hayaki a kasashe masu tasowa, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Daga shekarar 2015 zuwa 2018, an yi safarar irin wadannan motoci miliyan 14 daga Turai zuwa wasu nahiyoyi, kuma an kai rabinsu Afrika ne.

An sayar da hudu daga cikin dukkanin biyar ga kasashe matalauta musamman a Afrika.

Kwararru sun ce kusan kashi 80 cikin 100 na motocin ba su cika ka’idar ingancin fitar da su zuwa wasu kasashe ba.

Baya ga haifar da hadurra, irin wadannan motoci kan taimaka wajen gurbata yanayi sannan suna ta’azzara sauyin yanayi.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya yi kira ga kasashen da ke fitar da irin wadannan kaya da ma wadanda ke karbarsu da su kara tsaurara matakai wajen shigo da motoci.

A yanzu kowa na iya mallakar mota domin akwai akalla mota biliyan daya da miliyan dari hudu da ke yawo a titunan fadin duniya.

Wata tsohuwar mota

Yawancin wannan na faruwa ne a kasashe masu tasowa da ke Afrika da Asiya da kuma Latin Amurka.

A sharhinsu na shekara uku, masu bincike sun gano cewa dokokin shiga da motoci a wasu kasashe 146 na duniya ba su da karfi sosai.

Wani bincike na biyu dangane da al’amarin da hukumar kula da muhalli ta Neitherlands ta gudanar, ya gano cewa yawancin motocin da ake shigar da su Afrika daga kasar lokacin aikinsu ya wuce.

“Abin da za mu ce kawai shi ne, cikin wadannan motoci miliyan 14 kashi 80 cikin 100 ba su da ingancin da ake kira Euro 4,” in ji Rob de Jong, daya daga cikin masu binciken.

Motocin China

A cewar masu binciken, wadannan motoci na da haɗari kuma suna dauke da datti.

Sun yi imanin cewa shigar da irin wadannan motoci ne ke kara haifar da hadurra a kasashen Afrika da dama da kuma nahiyar Asiya.

Sannan suna fitar da gurbataccen hayaki da kan taimaka wajen kara barazanar sauyin yanayi.

Haka abin yake a Zimbabwe.

A zahiri, kusan kasa 30 na Afirka ba sa iyakance shekarun mota, saboda haka, kowace irin mota daga kowane irin zamani za ta iya shigowa.

“Haka ma game da rashin cika ka’idojin kiyaye hanya da muhalli, an lalata adadi mai yawa kuma an cire muhimman kayan aikinsu.”

Kashi 54 cikin 100 na motocin, ana kai su Afrika ne ta Neitherlands.

Hukumomi a kasar na nuna damuwa game da lamarin, kana suna son bijiro da sabbin matakai domin dakile shi.

Morocco

“Kasar Neitherlands ba za ta iya shawo kan wannan al’amari ita kadai ba,” a cewar Stientje van Veldhoven, ministan muhalli na kasar.

“Don haka zan bukaci kasashen Turai su bijiro da matakin bai daya tare da hadin kai da kasashen Afrika don ganin motocin da suka cika ka’ida ne kadai kasashen Turai ke kaiwa Afrika.”

Morocco na kyale motocin da ba su haura shekara biyar ba ne shiga kasar, ita ma Kenya na da shekarun da ta iyakance ga motoci domin shiga kasar.

A matakin yanki kuwa, kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS wadda ke da mambobi 15, ta shimfida ka’idoji ga motocin da za’a shigar da su kasashen daga shekarar 2021.

“Ina ganin babu adalci a ce wadannan kasashen da suka ci gaba su rika kai motocin da ba su cika ka’ida ba zuwa kasashe masu tasowa,” in ji Rob de Jong.

A daya bangaren kuma me ya sa kasashen da ake shigar da motocin cikinsu ba za su sanya dokoki ba?.

Tushen Labari

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku