Connect with us

Featured

Sabuwar Wayar Zamani ta iPhone 12

Published

on

iphone-12

Kamfanin Apple ya tabbatar da cewa sabuwar wayar da zai fitar mai suna iPhone 12 ita ce wayar kamfanin ta farko da za ta yi amfani da fasahar intanet ta 5G.

Kamfanin ya kuma ce za a ƙera ƙaramar wayar wadda ake kira “Mini” da girman fuskarta ba zai wuce inci 5.4.

Kamfanin na Amurka ya samu kasuwa matuƙa a wannan shekarar sakamakon ƙarin kasuwar da ya samu na sayar da wayoyin.

Masana kimiyya sun bayyana cewa sabuwar fasahar ta wannan wayar za ta bai wa kamfanin damar ƙara haɓaka matuƙa fiye da 2014, bayan kamfanin ya saki samfarin iPhone 6.

“Fasahar 5G za ta bayar da damar sauke abubuwa da kuma turawa cikin sauri, da kuma kallon bidiyo mai ingancin hoto kuma cikin sauri,” in ji Tim Cook, shugaban kamfanin.

Babu Cajar waya

Sabuwar wayar ta iPhone 12 za ta kasance mai babbar fuska fiye da sauran na baya.

Sai dai a karon farko, ba za a saka wa wayar caja da abin jin sauti na maƙalawa a kunne (earpiece) ba a cikin kwali. Apple ɗin ya ce amfanin wannan yunƙurin zai taimaka wurin rage tasirinsu ga muhalli.

Wani mai sharhi Dan Ives ya bayyana cewa kusan kashi 40 cikin 100 na wayoyin iPhone miliyan 950 da ake amfani da su ba a sabunta su ba, na kusan a ƙalla shekara uku da rabi, wanda hakan ya kawo wata damar.

Fasahar 5G

Kamfanin Samsung ne ya fara fitar da Fasahar 5G a wayar Galaxy S10 a Fabrairun 2019, sai kuma Huawei da OnePlus da Google su ma suka yi wayoyin masu 5G.

Sai dai masana sun ce da wuya kamfanin Apple ya zama shi ne na farko wurin fitar da wata sabuwar fasaha, har sai kamfanin ya jira ya ga fasahar ta nuna ƙwarai kafin ya fitar.

Kamfanin na 5G ya bayyana cewa a gwajin da ya yi, za a iya sauke bidiyo mai nauyin 20gig cikin daƙiƙoƙi 45.

Sai dai gargadin da kamfanin Apple ɗin ya bayar shi ne za a iya samun bambancin hakan sakamakon yankin da mutum yake da kumaƙarfin network ɗinsa.

Birtaniya ita ce ƙasa ta biyu daga Tarayyar Turai da ta fara amfani da fasahar 5G.

A Amurka – wadda ita ce kasuwa mafi girma ta Apple – intanet ɗin 5G ba shi da sauri. Wani bincike ya bayyana cewa sauke abubuwa a waya ta intanet ɗin 4G ya fi sauri fiye da 5G ɗin.

A wasu ƙasashen ma, har yanzu ma ba a sakar wa kowa da kowa 5G din ba ya yi amfani da shi.

Sai dai a ƙasar China – wadda ita ce kasuwa ta biyu mafi girma ta Apple, gwamnatin ƙasar ta bayar da ƙwarin gwiwar ƙara haɓaka fasahar a faɗin ƙasar, inda a kwanan nan ta bayyana cewa an samu cikakken sabis ɗin a Beijing da Shenzhen.

Tushen Labarin