Connect with us

Featured

SEC ta ce ta goyi bayan CBN akan haramta amfani da kuɗin intanet

Published

on

hukumar da ke kula da hannayen jari a najeriya

Hukumar da ke kula da hannayen jari a Najeriya, SEC ta ce ta goyi bayan Babban Bankin Najeriya kan haramta amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency.

A makon da ya gaba ne CBN ya ce ya dakatar da amfani da kuɗin na intanet da dangoginsa sannan ya umarci bankuna su rufe duk wasu asusu da ke aiki da kuɗin na intanet.

A wata sanarwa da ya fitar, SEC, wanda a baya ta taɓa nuna a shirye take ta amince da kuɗin intanet, ta ce ba za ta amince da shi ba a yanzu har sai tsarin bankunan Najeriya ya samar da hanyar amfani da kuɗin inatent yadda ya kamata – kamar dai yadda CBN ya ce.

CBN ya sa haramcin ne bisa zargin amfani da kuɗin intanet wajen almundahana da ta’addanci.

Haramcin ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya kuma wasu na ganin zai jawo koma baya a tattalin arziƙin ƙasar, ganin cewa Najeriya ce ƙasa ta biyu da ta fi amfani da kuɗin intanet kamar bitcoin.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku