Connect with us

Labari

Shafin Facebook ya toshe wasu dandazon masu kutse ta intanet

Published

on

shafin facebook ta toshe dandazon masu kutse

Kamfanin Facebook ya bayyana cewa ya toshe wasu dandazon masu kutse ta intanet a China waɗanda suka yi ƙoƙarin yin leƙen asiri ga ƴan gwagwarmaya da ƴan jarida ta hanyar saka musu manhajar leƙen asiri a na’urorinsu.

Kamfanin na Facebook ya ce gungun masu kutsen wanda aka fi sani da Earth Empusa ko kuma Evil Eye.

A cewar kamfanin sun yi niyyar kutsen ga kusan mutum ɗari biyar kuma akasarinsu waɗanda aka so yi wa kutsen, ƴan ƙabilar Uighur ne daga yankin Xinjiang na China waɗanda suke zama a ƙasashen ƙetare.

Kamfanin na Facebook ya ce masu kutsen sun ɓullo da wata hanyar yaudara, inda suka fake a matsayin ƴan jarida da ɗalibai da masu kare haƙƙi, inda suka yi ƙoƙarin ƙulla abota da waɗanda suke hari.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku