Connect with us

Shafukan Zumunta

Shafin Instagram ya ɗauki mataki kan masu mu’amula da yara ƙanana

Published

on

shafin instagram ya ɗauki mataki kan masu mu'amula da yara ƙanana

Instagram ya sake bijiro da sabbin matakan tsaro domin kare yara da ke karbar saƙonni da ba su dace ba daga Manya.

Manya da tsofaffi za su iya aika sako kaɗai ne ga yaran da ke bin shafinsu.

Sannan saƙonnin za su dinga ankarar da yara cewa ba lallai su saurari ko mayar da martani ba muddin hankalinsu bai kwanta da wanda ya aike musu sako ba.

Matakin zai yi aikin ne kawai idan shafin na dauke da bayanin shekarun mutum na asali, wanda dama a galibin lokuta yara na karyar shekaru wajen cike bayanansu a shafin Instagram saboda kar a taƙaita iya abin da za su iya yi ko shiga.

Kazalika, ana samun mutanen da ke rage shekarunsu a shafin.

Instagram ya ce yana kirkirar wata sabuwar fasaha da za ta taimaka wajen daƙile ko tantance ainihin shekaru, musamman ga wadanda aka fuskanci bayanansu akwai rashin gaskiya.

Shafin da ba kowa ke iya shiga ba (Private account)

Shekara 13 ita ce mafi kankanta na samun damar amfanin da shafin Instagram.

Shafin ya ce a yanzu zai ba yara zaɓin mayar da shafinsu na sirri wanda sai da izini za a iya shiga lokacin kirkirar ko yin rajistar soma amfani da shafin.

“Idan yara suka ƙi zaɓin shafin ‘sirrin’ lokacin rajista, zamu tura musu saƙo daga baya, mu sanar da su muhimmancin shafinsu ya kasance wanda ba kowa ke iya shiga ba sai da izini da tunatarda su, su duba wajen tsari wato “settings” a turance, a rufe ya ke.

A watan Janairu shafin TikTok shi ma ya fito da irin wannan tsarin.

  • Dole duk mutumin da shekarunsa ke ƙasa da 17 shafinsa ya zama na sirri sai da izini za a iya shiga.
  • Sannan yara ƴan shekaru 13 zuwa 15 dole su zaɓi mutanen da za su shiga shafinsu da iya tsokaci wato ‘comments’ da kuma zaɓin idan suna son ake ganin bidiyon da suke wallafawa a zaure.

Birtaniya ta bijiro da daftarin da zai sa ido da hukunta wadanda suka nuna gazawa wajen kare yara a shafukan intanet – ana dai sa ran dokar ta soma aiki kafin 2022.

Tushen Labari

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku