Connect with us

Fasaha

Tashoshin Radio na asali da Kuma Online Radio

Published

on

Tashoshin Radio na asali da Kuma Online Radio

Bambancin da ke tsakanin Tashoshin Radio na asali da Kuma tashoshin zamani na intanet (Online Radios).

Bunkasar sadarwar intanet a duniya ya sauya tsarin yadda ake yada shirye-shiryen radio a fadin duniya baki daya. Tsarin yada labarai da shirye-shiryen na intanet ya sha bamban da tsarin tashoshin yada labarai na asali wanda suka hada da AM da FM.

Tsarin farko na kafafen yada labarai, har yanzu ana amfani dashi. Fitowar tsarin yada labarai da shirye-shirye ba zai danne ko hana amfani da su ba. Hasali ma karin inganci ne ga tsarin AM da FM wajan kara fadadawa da kara nisan zango a fadin duniya baki daya.

Tsarin yada shirye-shirye na zamani wato Online Radio ko Internet Radio, basa bukatar amfani da akwatin radio domin kama tasha da sauraron su. Suna yada dukkan al’amuran su kai tsaye ta internet (streaming). Kuma a  farkon fitowar Internet Radio ana amfani da Kwamfuta da manyan wayoyin Zamani (smartphones) domin kamawa da sauraron su ta hanyar amfani da manhajoji ko kuma adreshi kai tsaye.

Gidajen Radio na asali suma sukan yi amfani da wannan fasaha ta internet Radio domin yada dukkan shirye-shiryen su a fadin duniya baki daya. Za kaji a kullum lokacin gabatar da shirye-shirye suna snar da masu sauraro cewa “Za ku iyasauraron tashar mu a duk inda kuke a fadin duniya ta shafin gidan radion ko ta manhajar TuneIn da sauran su…”. Saboda kada abarsu abaya.

Kuma a halin yanzu lokaci ya yi da kasuwar akwatinan radio ta fadi kasa warwas! Zamani ya kawo lokacin da aka fi amfani da wayoyi wajan kama tashoshin radio cikin sauki da sauti mai kyau, ba tareda kinkimar radio ana yawo ba, ko taruwa a kofar gida ko shago domin sauraron kayatattun shirye-shirye ko labarai.

Masana sunyi hasashen cewa nan gaba lokaci zaizo da tashoshin radio na zamani (online radios) za su shafe tashoshin radio na asali wato AM da FM. Kasancewar cigaban fasaha ya sanya ana iya kama tashohin online radios a cikin radion ababen hawa (Car Radios), Tashoshin tauraron dan adam (Satellite Radios/TV), Agogon Zamani (Smart Watch) da sauran su.. Kuma mai sauraro yanada zabin sauraron shiri ko wakokin da yake da bukakata daga online ko internet radio.

Akan tsara online radio yadda kowa zai iya ganin jadawalin shirye-shiryen tashar da kuma jerin wakoki domin masu sauraro. Sabanin yadda tashoshin radio na asali ke gabatar da shirye-shiryen su.

Idan za akafa tashar radio ta asali, ana da bukatar gine-binen ofis-ofis da dakunan gabatar da shirye-shirye (Studios) da kuma fili domin kafa babban turken yada shirye-shirye (Radio Mast ko Antenna), injin bada wutar lantarki da sauran na’urori masu yawan gaske, sannan kuma uwa uba lacici gidan radio (License). A takaice akwai bukatar kudade masu yawa domin kaddamar da tshar radio na asali AM da FM. Bayan haka kuma akwai bukatar daukar kwararun ma’aikata na bangarori daban daban domin gudanar da aiyukan radio baki daya.

A tsari irn wanda fasaha ta kawo na online ko internet radio abubuwanda ake bukata basu kai na gidajen radio na sali ba. Hasali ma a cikin daki ko shago za’a iya kaddamar da shi. Kuma ba a kashe kudi kamar wancan. Duk dacewa akwai na’urori masu tsada da kuma masu sauki da za’a iya amfani da su, wato iya kudin ka iya shagalin ka. Mutum daya zai iya sarrafawa da gudanar da online radio, da kwamfutar sa daya ko fiye da haka, da kuma manhajoji, da sadarwa intenet da sauran su… A wasu lokutan akan kira su da suna web radios.

Fasaha ta shiga kowanne bangare na wadannan kafafen yada shirye-shirye. Kuma har yanzu tana taka rawa a fannin tashoshin yada labarai da shirye-shirye domin kawar da matsaloli, inganta sauti da sauran su… Idan muka duba zamu ga cewa tashoshi radio masu gabatar da shirye-shiryen su akan zangon FM sun fi yawa a halin yanzu saboda yadda fasaha ta kera na’urorin su a matakai daban-daban yadda za a iya mallakar su cikin sauki a fadin duniya. Tashoshin AM kuma zamu ga cewa basu da yawa saboda girma da tsadar na’urorin su, kusan mallakar su sai Gwamnatoci.

A karshe , lokaci ne kawai zai bayyana matsayin kowanne daga cikn wadannan kafafen yada shirye-shirye, da kuma yadda fasaha ta ke tankade da rairaya wajan sauya dukkan al’amura.

Continue Reading