Connect with us

Featured

Tik Tok: Matasan da aka tsare saboda bidiyon rashin kunya

Published

on

Matasan da aka tsare
Mawada na cikin masu karfin fada a ji a TikTok da aka cafke saboda dalilai na ''rashin da'a''

Bayanan hoto, Mawada na cikin masu ƙarfin faɗa a ji a TikTok da aka cafke saboda dalilai na ”rashin ɗa’a”

”Abin ya zo mana da mamaki. Ba ta yi wani abu ba mara kyau ba – ‘yar uwata ba ta aikata manyan laifuka. Burinta shi ne ta yi fice a san ta,” a cewar Rahma, babbar yayar Mawada Al Adham, mai ƙarfin faɗa a ji a shafukan sada zumunta, da aka yanke mata shekaru biyu a gidan kaso.

Mawada, mai shekara 22 ɗalibar jami’a ce da aka yanke mata hukuncin zaman gidan kaso kan laifin karya dokokin al’adun iyalai na ƙasar Masar.

A watan Mayun da ya gabata aka cafke ta bayan wallafa wani bidiyo a manhajar TikTok da Instagram da ke nuna tana bi bin kan wakar wani fitaccen mawaƙi da taka rawa cikin wasu haɗaɗɗun kayan gayu.

Masu shigar da ƙara sun ce ta nuna rashin ɗa’a a bidiyon.

”Mahaifiyarta ba ta iya motsawa daga kan gadonta. Kullum tana cikin kuka. Wasu lokutan tana tashi cikin dare ta tambaya ko Mawada ta dawo gida,” a cewar Rahma.

Ƴan matan TikTok’

Haneen Hossam ita ma fitacciya ce a shafukan sada zumunta

Bayanan hoto, Haneen Hossam ita ma fitacciya ce a shafukan sada zumunta

Mawada na daya daga cikin ‘yan mata biyar da aka yanke wa irin wannan hukunci na zaman gidan yari, da kuma tarar kusan dala dubu 20.

Ƴan matan biyar da suka yi fice a matsayin ”Yan matan TikTok’ sun hada da wata fitacciya ita ma a shafukan sada zumunta, Haneen Hossam, da kuma wasu uku da ba a bayyana sunansu ba.

Rahma ta ce Ƙanwarta tana tallata kayan Ƙawa a shafukan sada zumutan ga manyan fitattun kamfanoni. ”Kawai dai ta kasance mai buri sosai. Ba ta da buri daya wuce ta zama jarumar fina-finai.”

A cewar Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty, masu shigar da Ƙara sun yi amfani da hotunan 17 na Mawada a matsayin hujjojin nuna ”rashin ɗa’arta”.

Mawada ta ce waɗannan hotunan an kwashe su ne daga wayarta ba tare da saninta ba lokacin da aka sace wayar a bara.

Me ya sa ita?’

'Yar'uwar Mawada ta ce ta shiga yanayi na dimauta bayan jin hukuncin

Bayanan hoto, ‘Yar uwar Mawada ta ce ta shiga yanayi na ɗimauta bayan jin hukuncin

A ranar 17 ga watan Agusta za a saurari ɗaukaka ƙara kuma Rahma na sa ran ƙanwarta aƙalla ta samu sassaucin hukunci.

”Me ya sa ita?! Wasu matan da ke irin wannan harka, na yin abin da zarce hakan. Babu wanda ya hukunta su,” ta yi waɗannan tambayoyi a cikin fushi.

Mawada ta suma a lokacin da ta ji hukunci da aka yanke mata da farko, a cewar lauyanta, Ahmed Bahkiry. ”Ta shiga kaduwa sosai – ba a fayyace irin tuhume-tuhume da ake yi mata ba.”

”Gidan yari ba mafita ba ce, ko da a ce wasu daga cikin bidiyonta sun saba doka da al’adunmu,” a cewarsa. ”Gidan yari na ɓata mutum. Mahukunta na iya musanya gidan yari da cibiyar gyara hali.”

Continue Reading