Connect with us

Shafin Intanet

Tushen Samun Kudi a Intanet

Published

on

Tushe da hanyoyin samun kudi a intanet

Tushen Samun Kudi a Intanet

Wannan batu ne da kullum ake bukatar karin bayani akan sa. Saboda yadda cigaban zamani ya kawo sauye-sauye a bangarori masu yawa na gudanar da aiyukan yau da kullum a duniya baki daya. Haka zalika fasahar zamani ta kawo abubuwa masu yawa da mutum zaiyi amfani da su wajan samun madogara ta hanyar amfani da intanet.

Wannan dalili ya sanya shakku da mamaki a cikin zukatan jama’a musamman wadanda suke da karancin fahimta ga al’amuran fasaha. Shakka babu ana samun kudi ta intanet. Akwai abubuwa masu yawan gaske da idan aka fahimce su har akayi aiki da su, lallai za’a kai gaci. Domin wasu Jama’a suna tsammanin kudin da ake amfani dashi wajan siyan data, daga cikinsa ne ake samun kudi a intanet, to ba haka bane. Kudin da aka sayi data domin shiga yanar gizo yana karewa ne akan amfanin da akayi dashi, kuma kamfanin sadarwar da akayi amfani da layin su, gare su kudin ke tafiya. Sannan wanda ya sayi datar shi kuma ya more kudin sa wajan watayawa a intanet.

Akwai babban al’amari da ake amfani da shi a intanet wanda shine tushen samun kudi a ko’ina bama a intanet kadai ba. Wannan abu kuwa shi ne; yawan mutane (Traffic). Ko a Kasuwa ta zahiri, yawan mutane shi ne babban al’amari dake amfanar da kowa. A wannan gabar nake tunasar da mai karatu wakar marigayi Dr. Mamman Shata inda yake cewa “Yawan Mutane Shi ne Kasuwa, ni ku rabani da tarin rumfuna”. Wannan batu na marigayi babu tantama, tunda  gashi Allah ya kawo mu zamanin da ake amfana daga yawan mutane a shafukan intanet domin samun kudi.

Mai karatu, idan ka nutsu kayi tunani mai zurfi zaka ga cewa a kullum ta Allah Jama’ar duniya suna tururuwa wajan shiga shafukan intanet domin sanin mai duniya take ciki, neman ilimi, sada zumunci, siye da siyarwa, bincike da sauran su… hakan yana faruwa ne ta fuskar fasaha, har takai ana cewa duniya ta zamo tamkar a tafin hannu.

Akwai shafuka masu yawan gaske a intanet wadanda kowanne yana da tsarin sa da kuma dalilai na kasancewar sa. Idan muka dauki shafin zumunta na Facebook wanda yayi shuhura  a duniya, duk da cewa akwai manyan shafuka irin su google, yahoo da sauran shafuka makamantansu da yawa a intanet, da kuma yadda manyan kamfanoni da masana’antu na duniya suka zuba jari a cikin sa, har takai ta kawo ana saka shi a matsayin shafi na biyu a duniya da akafi samun kudi ta cikin sa.

Jama’ar da suke dandazo wajan ziyartar shafukan intanet shine babban sirri kuma shine tushen samun kudin a intanet. Amma har yanzu wasu jama’a da yawa basu san cewa tuni anyi musu nisa ba, musamman arewacin Najeriya. An barmu da lika hotuna a shafuka domin burgewa da gwalli, sai yawan downloading na tarkace,mafi yawan cin su marasa amfani.

Ta yaya za’ayi na samu yawan Jama’a a shafi na domin nima na sami kudi ta intanet?

Wannan tambaya ce mai muhimmancin gaske, wadda ke bukatar amsa gamsashshiya. Kamar haka;

  • Mallakar Shafi a Intanet: Na kashin kai (Profile), na Kasuwanci, fadakarwa, ilimantarwa da sauransu… Shine matakin farko domin shiga tsarin samun kudi a intanet. Anfi so adreshin ya kasance mai ma’ana da alaka da kayan cikin shafin sannan ya zamo mai saukin fada da rubutawa.
  • Sabuntawa akai akai: Sabunta al’amuran shafi akai akai shi ne babban dalilin dake jawo hankalin  maziyarci domin karantawa ko duba sababbin al’amura a kowanne lokaci har shafin ya zamo kamar wajan daukar darasi, ko siye da siyarwa, ko wajan bincike da sauran su… rashin sabuntawa yana rage zuwan maziyarta har ma su dai na zuwa.
  • Wallafar Asali: Ana son duk abubuwan da za’a wallafa a cikin shafi ya kasance nan ne asalin sa, ba a wani shafi aka dauko shi ba. Idan kuma an dauko daga wani shafi ne to ya kasance dan kadan, kamar layi 2 ko 3 sannan kuma a rubuta adreshin asalinsa wato inda aka dauko shi.
  • Kulawa da maziyarta akan lokaci: Nuna kulawa da damuwa ga dukkan bukatun maziyarta. Amsa tambayoyin su a duk lokacin da suka tuntubi jam’in shafi, da kuma basu kulawa yayin mu’amala da shafin musamman idan suka sami tangarda a shafin.

Wadannan abubuwa kadan ne daga cikin abubuwan da suke jawo dandazon maziyarta ga shafukan intanet. Wanda idan yawan maziyartan ya kai wani adadi mai daraja, da kuma cika dukkan ka’idodi da sharuddan da aka shimfida domin shiga tsarin samun kudi a intanet, shikenan sai farin ciki.

Continue Reading