Connect with us

Labari

Twitter: An dakatar da shafin Twitter a Najeriya

Published

on

an dakatar da shafin twitter a najeriya

Shafin Twitter ya daina aiki a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a ranar Juma’a.

An lura shafin ya daina aiki ne a tsakiyar daren Juma’a wato wayewar garin ranar Asabar.

Hakan na faruwa ne sa’o’i kadan bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin na Twitter.

Wata sanar da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta fitar, ta ce Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Minista Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.

Lai Mohammed ya kuma ce ya bai wa hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasar NBC ta fara shirye-shiryen ba da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.

Sai dai gwamnatin Najeriyar ba ta fayyace abin da take nufi da wannan mataki ba ya zuwa yanzu.

Bayanan bidiyo,

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shafin Twitter ya goge wani saƙo cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa yana gargaɗin ƴan awaren IPOB.

Tun bayan cire saƙon shugaban ƙasar fadar Shugaba Buhari ta ce tana sane da matakin da Twitter ya ɗauka, kuma ta aika da buƙatar neman jin dalilin da ya sa kamfanin ya goge saƙon.

Tuni dai kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce za ta kalubalanci matakin gwamnatin a kotu, a wani sako da ta wallafa a Twitter din.

Sakon Buhari

Wannan shine saƙon da shafin Twitter ya goge na Shugaba Buhari

 

Shafin ya daina aiki

Bayanai sun nuna cewa shafin na Twitter ya daina aiki a kasar ta Najeriya tun daga tsakar daren Juma’a.

‘Yan kasar da ke amfani da shafin sun kasa bude shi ta hanyar da aka saba, ko da yake akwai wata dabara da ake amfani da ita ta hanyar VPN domin iya bude shafin.

Sai dai ba kowa ne ya san yadda ake yin hakan ba.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Jim kaɗan da fitar da wannan sanarwa sai ƴan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta musamman Twitter.

Tuni aka ƙaddamar da maudu’ai har huɗu a shafin na Twitter don tattaunawa kan batun, da suka haɗa da #So Twitter da aka yi amfani da shi kusan sau miliyan ɗaya a ƙasa da ɗaya da #Twitter in Nigeria 100,000, da #Using Twitter da aka yi amfani da shi sau 239,000.

Sannan akwai maudu’in #Federal Government mai 36,000 da kuma #TwitterBan mai saƙonni 1,384. AKwia kuma irin su #Jack da #Lai Mohammed da #Twitter in Nigeria da #Suspending Twitter da dai sauran su.

Ƴan ƙasar da dama ne suka dinga bayyana ra’ayoyi daban-daban kamar haka:

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP a 2019 Alhaji Atiku ya wallafa cewa: “Ina fatan kar wannan ya zama saƙona naƙarshe a Twitter.”

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Jibrin Ibrahim tsohon shugaban Cibiyar Binciken Harkokin Dimokraɗiyya CDD shi ma ya rubta: “Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed, ya dakatar da Twitter a Najeriya saboda a cewarsa ana amfani da kafar wajen raba kan ƴan ƙasar. To hakan yana nufin idan babu Twitter ana da tabbacin kan ƴan ƙasar zai haɗu ne?”

Tsohon sanatan yankin Kaduna Ta Arewa Sanata Shehu Sani ma cewa ya yi: “Dakatar da Twitter, jawowa kai abin faɗa ne.”

Arewa Twittér kuwa cewa ya yi: “Ina goyon bayan wannan dakatarwa duk kuwa da cewa ina samun kuɗ a Twitter, amma wannan ne mataki mai kyau da gwamnatin tarayya ta dauka da ya birge ni.”

Kauce wa Twitter, 2

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku