Connect with us

Labari

Wani babban attajiri na neman mutum takwas da su raka shi zuwa duniyar wata

Published

on

yusaku maezawa na gayyatar mutum takwas daga ko ina afadin duniya don su raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa duniyar wata

Wani hamshakin attajiri dan Japan Yusaku Maezawa yana gayyatar mutum takwas daga ko ina afadin duniya don su raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa duniyar wata a jirgin SpaceX flight na Elon Musk.

“Ina son mutane daga ko ina su nemi yin wannan rakiya,” kamar yadda ya fada a wani bidiyo da ya wallafa a Tuwita, inda ya kuma wallafa adireshin intanet din da za a shiga a nemi aikin rakiyar.

Ya ce shi zai dauki nauyin gaba daya tafiyar, don haka ‘yan rakiyar a garabasa za su je.

An sanya lokacin bulaguron mai taken dearMoon, ne a shekarar 2003.

Wadanda za su nemi wanan rakiya na bukatar cika wasu sharuda biyu: sai sun kasance duk abin da suke na taimakon al’umma ne a wani fannin, kuma sai idan suna da burin taimakon sauran abokan tafyar da suke da irin wannan buri, in ji shi.

“Na sayi dukkan tikitin jirgin, don haka zai kasance tafiya ce ta kashin kai,” ya kara da cewa.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Mr Maezawa, hamshakin mai arzikin a fannin kayan kawa, kuma fasihi, a baya ya ce ya shirya gayyatar fasihai don yin tafiyar tare, amma sai aka gyara tsarin ta yadda mutane daga sassan duniya daban-daban za su samu damar bin jirgin.

“Idan kana kallon kanka a matsayin fasihi, to kai fasihi ne,” a cewarsa.

A bara, ya kaddamar da wani shiri na neman sabuwar budurwar da za ta raka shi a bulaguron, kafin daga bisani ya fasa saboda tunani daban-daban.

A shekarar 2018, an ambaci Mr Maezawa a matsayin fasinjan farko mai zaman kansa da zai yi zagaye a duniyar wata a jirgin SapceX, na kamfanin Elon Musk.

Ba a bayyana yawan kudin da Mr Maezawa zai biya na tikitin jirgin ba, amma Elon Musk ya ce makudan kudade ne.

Shirin zuwa duniyar wata na 20223 shi ne zai zama na farko da dan adam zai yi tun bayan shekarar 1972.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku