Connect with us

Kimiyya

Wasu Kasashe sun dakatar da yin allurar rigakafin Covid – 19

Published

on

denmark, norway da iceland sun dakatar da allurar astrazeneca na wani lokaci

Kasashen Denmark, Norway da Iceland sun dakatar da allurar AstraZeneca na wani lokaci.

kasashen Denmark, Norway da Iceland a ranar Alhamis sun ɗan dakatar da yin amfani da allurar ta AstraZeneca ta Covid-19 kan damuwar marasa lafiya da ke ci gaba da daskarewar jini, kamar yadda masana’anta da masu kula da magunguna na Turai suka dage cewa allurar ba ta da wata illa.

Kasar Denmark ce ta fara sanar da dakatarwar, “biyo bayan rahotannin da ke nuna yadda lamarin ya shafi zubar jini” a tsakanin mutanen da suka karbi allurar, in ji Hukumar Lafiya ta kasar a cikin wata sanarwa.

Ta kara jaddada cewa yin hakan rigakafi ne, kuma “ba a tantance ba, a halin yanzu, cewa akwai alaka tsakanin allurar rigakafin da kuma daskarewar jini”.

Ya zuwa ranar 9 ga Maris, an bayar da rahoton daskarewar jini 22 tsakanin mutane sama da miliyan uku da aka yi wa rigakafi a Yankin Turai, in ji Hukumar Kula da Magunguna ta Turai (EMA).

Kasar Austria ta sanar a ranar Litinin cewa ta dakatar da amfani da allurar rigakafin AstraZeneca bayan da wata ma’aikaciyar jinya mai shekaru 49 ta mutu sakamakon “matsaloli na daskarewar jini” kwanaki bayan da ta sha wani magani akan Covid 19.

Sauran kasashen Turai hudu – Estonia, Latvia, Lithuania da Luxemburg – suma sun dakatar da amfani da alluran rigakafi daga wannan rukuni, wanda aka tura zuwa kasashen Turai 17.

Amma duk da haka Denmark ta dakatar da amfani da dukkan abubuwan da take samarwa na AstraZeneca, kamar yadda Iceland da Norway suka yi a sanarwar da suka yi a ranar Alhamis saboda nuna damuwa irin wannan.

A ranar Laraba, EMA ta ce binciken farko ya nuna cewa yawancin maganin alurar rigakafin AstraZeneca da aka yi amfani da su a kasar Austria da alama ba za a dora alhakin mutuwar ma’aikaciyar lafiyar ba akan rigakafin.

“Wannan hanya ce ta taka tsantsan dangane da wasu rahotanni a Turai,” in ji Stephen Evans, farfesa a fannin ilimin magunguna a Makarantar Kula da Tsafta da Magungunan Tropical.

“Daidaito tsakanin haɗari da fa’idar har yanzu ya ta’allaka ne da fa’ida allurar,” in ji shi.

AstraZeneca, wani kamfanin Anglo-Sweden ne wanda ya kirkiro allurar tare da Jami’ar Oxford, ya kare lafiyar samfurin sa.

“An yi karatu mai zurfi akan allurar sosai a cikin gwaji na asibiti abisa mataki na uku kuma bayanan da aka yi nazari a kansu sun tabbatar da cewa an yi amfani da allurar gaba daya sosai,” in ji mai magana da yawun kungiyar ya shaida wa AFP.Birtaniyya, wacce yaduwar allurar rigakafin ta AstraZeneca ta goyi bayanta sosai, ta kuma kare ta da cewa “mai lafiya ce kuma mai tasiri”.

Dakatarwar da Danmark din, wanda za a sake duba shi bayan makonni biyu, ana sa ran zai kawo tsaiko a aikin rigakafin kasar. Kasar Denmark yanzu tana sa ran a yiwa daukacin mutanen da suka manyanta rigakafin kafin tsakiyar watan Agusta maimakon farkon watan Yuli, in ji hukumar lafiya.

Fira Minista Mette Frederiksen ta ce “Tabbas muna bakin cikin wannan lamarin.”

Frederiksen, wanda ya yunkuro don samar da karin alluran rigakafin kuma ya kulla kawance mai sabani da Austria da Isra’ila don yin hakan, ya kare hukuncin da hukumomin lafiya na Denmark suka yanke.

Ta shaida wa manema labarai cewa “A koyaushe akwai hadari da ke tattare da alluran rigakafin.”

“Abubuwa sun tafi daidai a Denmark, amma akwai wasu haɗarin da ke da nasaba da rigakafin AstraZeneca da ke buƙatar yin bincike sosai. Wannan a gare ni ita ce hanya madaidaiciya da za a ci gaba.”

Daraktan Hukumar Lafiya ta Denmark Soren Brostrom ya jaddada cewa “ba mu daina amfani da allurar ta AstraZeneca ba, kawai mun dakatar da amfani da shi ne”.

Brostrom ya ce “Akwai manyan takardu da ke tabbatar da cewa allurar rigakafin tana da inganci da tasiri.”

“Amma da mu da kuma Hukumar Kula da Magunguna ta Denmark dole ne mu yi aiki a kan bayanai game da yiwuwar mummunar illa, a Denmark da sauran ƙasashen Turai.”

Denmark ta ce mutum daya ya mutu bayan karbar allurar. EMA ta ƙaddamar da bincike game da mutuwar.

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku