Connect with us

Shafukan Zumunta

Yadda ake kaddamar da matakin tsaro na 2FA a shafukan zumunta

Published

on

fasahar tsaro ta 2fa

Yadda ake kaddamar da matakin tsaro na Two Factor Authentication (2FA) a shafukan zumunta.

Wannan fasaha ta two factor authentication tsari ne da yake kara rubanya (multiply) karfin matakan tsaro a shafukan zumunta, wanda yake magance matsalar kutse da kwacen ragamar gudanarwa daga masu ita na asali (user account administration). Dogaro da password kawai baya hana gamuwa da matsaloli musamman password mai sauki ko mai rauni.

Jama’a da yawa sukanyi amfani da password guda a dukkan mu’amalar su a shafukan intanet, wanda yin hakan ya bawa masu kutse damar cimma burin ‘yan fashi da kwace harma da satar bayanan sirri a intanet.

Amfani da wannan sabuwar fasaha ta Two Factor Authentication yana taka rawa wajan tsaurara tsaro bayan password. Wannan tsari yakan aika sakon na lambobi guda 6 ta waya domin tantancewa, kafin a sami damar shiga (login) shafin da ake da bukata. Wannan fasaha na da sukin aiwatarwa kuma tana kwantar da hankulan masu amfani da shafukan zumunta, ta hanyar tsaurarawa da wahalar da masu aikin kutse a intanet. Yana hana su cimma burin su a shafukan da ake amfani da ita (2FA).

Saboda haka a halin yanzu kowa yana iya kaddamar da wannan fasaha a shafukan zumunta. Ga bayani akan yadda ake kaddamar da wannan matakin tsaron a shafukan zumunta kamar; Facebook, twitter, WhatsApp, Snapchat, Instagram da kuma LinkedIn.

Ga masu amafani da Facebook:

Da farko akwai bukatar Login wato a shigar da username da password, bayan an shiga sai a duba da kyau daga sama a nemi kalmar Settings a danna (click) bayan sashen settings ya bude, sai a nemi Security and Login wanda shine a sama daga bangaren hagu.

Sannan a gangara kasa har zuwa inda aka rubuta Use two-factor authentication,  sai a duba bangaren dama za’a aga kalmar Edit ita ma sai a danna (click). To daganan sai a duba da kyau, idan tun farko ba’ayi amfani da lamabar waya ba, to anan ya zama dole a shigar da lamabar waya sannan a latsa kalmar Enable. Idan kuma an saka lamba tuntuni kai tsaye sai a danna Enable.

Ga masu amafani da Twitter:

Anan ma za’a nemi kalmar Profile, sai a tafi kai tsaye zuwa ga Settings and Privacy. Daga nan sai a nemi kalmar Securty sai a nemi inda aka ce Set up login verification. Daga nan sai zabi tsarin aika sako ta lambar waya. Idan akabi tsarin dalla-dalla har ka kammala cikin nasara. Daga nan za’a dinga samun sako ta waya a duk lokacin login.

Ga masu amafani da Instagram:

Shima da farko za’a shiga Settings, daga nan sai a duba daga cikin jerin abubuwan dake wajan sai a danna Privacy and Security. Bayan an shiga Privacy and Security sai a zabi Two-Factor Authentication.  Daga nan sai zabi tsarin amfani da gajeren sako (text message), a saka lambar waya idan tun farko ba’a saka ba. Sai abi umarnin tsarin domin kammalawa.

Ga masu amafani da Snapchat:

Daga sashen Camera Home sai a danna kalmar Profile a bangaren hagu daga sama. Sannan a danna kalmar Settings idan an shiga sai a danna Two-Factor Authentication, sannan abi umarnin da tasrin ya bayyana domin kammalawa.

Ga masu amafani da WhatApp:

Domin kaddamar da two-step verification a manhajar WhatsApp. A nan ma a danna Settings, sannan a danna Account, sai a danna Two-step verification bayan ya bude sai a danna Enable. Kuma yanada kyau a kara da agreshin email domin samun sakon tsaro ko babu waya.

Ga masu amafani da LinkedIn:

Za’a danna kalmar Me wadda take a matsayin profile daga sama a bangaren dama. Sai duba daga cikin jadawalin shafin (menu) sai a Settings & Privacy. Daga sashen gudanarwa (Account section) sai a danna Login and Security. Sabon shafi zai bude sai a danna account kafin kalmar Privacy (Sirri). Daga nan sai a kunna (turn on) Two-step verification idan ba a saka lambar waya ba tunda farko, sai ayi kokarin shigar da lambar waya a lokacin. Sai a bi umarnin dake biye domin kaddamar da wannan tsaro.

Bugu da kari, a kowanne shafi ko manhajar zumunta akwai damar samun lambobi masu yawa akan tsarin backup wadanda za’a iya rubutawa a takarda ko boyewa domin gudun ko ta kwana. Saboda waya zata iya faduwa ko a dauketa. Idan haka ta faru sai ayi amfani da wadanda aka adana.

Da fatan Allah ya amfanar damu, ya kuma tsare mu.