Connect with us

Kimiyya

‘Yan Sama jannati da masu ninkaya a ruwa na fuskantar barazanar tsukewar zuciya

Published

on

Tsukewar Zuciya

Shafe tsahon lokaci a cikin jirgin sama jannati zuwa duniyar wata na da kamanceceniya da matsalar da daɗewa cikin ninkaya ke haddasawa, duka biyun za su iya janyo motsewar zuciya.

Wannan shi ne sakamakon binciken da masana suka yi, inda suka danganta shi da mai shafe shekara a duniyar wata Scott Kelly da dan wasan ninkaya Benoît Lecomte.

Dukkansu biyun suna takura zuciyoyinsu, ta yadda ake barin ta da tarin nauyin da ke haddasa mata motsewa.

Motsa jiki kadai ba zai iya janyowa zuciya sauye-sauye ba.

Binciken da Dr Benjamin Levine ya jagoranta, wanda farfesa ne a fannin likitanci a Jami’ar Texas da ke Dallas, an buga shi a mujallar kiwon lafiya.

Biciken ya bayyana illar dadewa a duniyar wata, kamar nisan zuwa duniyar Mars wanda ake shirin zuwa nan da gomman shekaru.

Farfesa Levine kuma darakta a cibiyar motsa jiki da ilimin muhalli, da hadin gwiwar fannin kiwon lafiya na Texas, ya shaida wa Manema Labarai cewa; ”Daya daga cikin abubuwan da muka gano cikin shekarun da muka yi muna bincike, shi ne zuciya kamar roba take.

Don haka zuciya na sabawa da nauyin da aka dora mata.”

Scott Kelly

Bayanan hoto: Rashin iska mai rike abubuwa a zuciyar Scott Kelly za ta haddasa tsukewar zuciya – Asalin hoton, NASA

“Wani abu da ke faruwa a cikin jirgin da ke zuwa duniyar wata, shi ne babu isasshiyar iskar da ke sanya jini gudana, saboda ba ka samun isasshiyar iskar da ke riƙe abubuwa.”

Scott Kellyya shafe kwanaki 340 cikin jirgin ISS da ke zuwa duniyar wata, don bai wa masana kimiyya damar yin nazari kan illar doguwar tafiyar ga rayuwar dan adam.

A ranar 5 ga watan Yuni 2018, shi ma Benoît Lecomte ya fara ninkaya a tekun Pacific inda a baya tekun Atlantic ya je.

Ya yi ninkaya ta kilomita 2,821 cikin sama da kwanaki 159, daga baya ya yi watsi da yunkurin.

Shafe dogon lokaci ana ninkaya na sauya nauyin da ake dorawa zuciya na iska, saboda mutum na tafiya ne a miƙe maimakon a kwance.

A kowacce rana, Lecomte ya na ninkayar kilomita 5.8 cikin sa’a, yana baccin sa’a kusan takwas kowanne dare. Hakan na nufin yana kwashe tsakanin awa 17 a kowacce rana yana ninkaya.

Masana kimiyya kan yi amfani da lokacin hutu don yin nazarin yanayin sararin samaniya cikin jirgin da ke zuwa duniyar wata, saboda kwanciya a mike yana kara iska mai rike abubuwa da ragewa zuciya nauyi.

Amma Farfesa Levine ya ce ninkaya mai tsaho a cikin ruwa a mike ya fi, maimakon a dunkule.

Ben Lemonte ya na ninkaya a cikin teku

Bayanan hoto: Ben Lemonte ya na ninkaya a cikin teku – Asalin hoton, Reuters

Saboda jinin dukkan mazan biyu mai ninkaya da mai zuwa duniyar wata ba ya gudana yadda ya dace, don haka zuciyarsu za ta fara motsewa.

”Idan mu ka duba bangaren hagu na zuciya, zamu ga yadda ta rasa kashi 20 zuwa 25 cikin 100 na rashin gudanar jini yadda ya dace cikin watanni 4 zuwa 6 na lokacin Mista Lecomte ya ke ninkaya,” in ji Dakta James MacNamara, wanda shi ma ke aiki a cibiyar binciken kimiyya ta Texas.

“Mun kuma ga yadda jini baya gudana yadda a ya dace a jikin Kaftin, da kashi 19 zuwa 27 cikin 100 a shekara guda.”

Harwayau yawan motsa jiki ba bisa ka’ida ba, na janyowa zuciya motsewa. Duk da haka yawan motsa jikin bai kai yadda zai kare zuciyar kaftin Kelly daga motsewa ba, in ji masana kimiyyar.

A farkon nazarin, masu binciken sun yi mamakin yawan motsa jikin da Mista Lecomte yake a cikin ruwa, ta yiwu ya kare zuciyar daga motsewa.

“Duk da cewa na yi tsammanin zuciyar Ben ba za ta tsuke ba. Wannan shi ne abin da ya fi ban sha’awa game da kimiyya, ka na karuwa kan abin da ka ke nazari a kai, musamman gano abin da ba kai tsammani,” in ji Farfesa Levine.

Mista Lecomte yana amfani da kafafunsa wajen motsawa a cikin ruwa idan ya na ninkaya.

“Babu abubuwa masu yawa. Kuma rashin ayyukan motsa jiki ba sa bai wa zuciya kariya daga rashin iskar aiwatar da,” in ji Farfesa Levine.

Haka kuma abubuwan da zuciya ke dauka ba sa dadewa, duka zukatan mazajen biyu na komawa daidai da zarar sun dawo rayuwarsu ta yau da kullum, ma’ana babu zuwa duniyar wata ko ninkaya.

Sai dai jijiyoyin da jini ke gudana a cikin zuciya, su na kara budewa idan ana duniyar wata saboda yanayin ya ke ya na kara fadada zuciya.

Wannan yanayin shi ya ke sanya zuciya bugawa da sauri-da-sauri ba kamar yadda ta saba ba, hakan ka iya sanya mutum cikin hadarin kamuwa da shanyewar barin zuciya.

Akwai kuma wani karin hatsarin, saboda yawan tiririn da ake da shi a duniyar wata ka iya haddasa matsanancin ciwon zuciya.

Ana tantance masu zuwa duniyar wata kan ciwon zuciya, ko da yake an fi danganta matsalar da masu matsakaita da yawan shekaru.

Wannan yana da muhimmanci, saboda kamuwa da ciwon zuciya a duniyar wata ka iya zama mummunan yanayi.

Tushen Labari

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku