31 C
Kano
Thursday, October 22, 2020

‘Yar Nijar ta farko mai aiki a hukumar NASA ta Amurka

Mafi Shahara

Mace ta farko masaniyar kimiya ‘yar kasar Nijar da ta samu aiki a Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Amurka a watan jiya, ta ce babban burinta shi ne yadda nan gaba za ta koma kasarta domin taimaka wa mata da matasa ta fuskar ilmin kimiya da cigaban rayuwarsu.

Dokta Fadji Zauna Hassan Maina mai shekaru ashirin da tara, haifaffiyar Zinder, kuma ta fara karatunta a Nijar kafin ta garzaya kasashen Turai.

Ta yi wa Umaymah Sani Abdulmumin ta BBC Hausa ƙarin bayani kan irin gwagwarmayar da ta yi.

Dr Fadji Maina ta NASA

Farkon rayuwarta

A Zinder na girma, kuma samun aiki a hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Amurka, NASA sai mutum na da ilimi sosai.

Sai da na sami digirin PhD a Faransa, kuma bacin shi na ƙaro karatu a Italiya kafin na taho nan Amurka.

A ƙokarinki na cimma burinki, mene ne abin da yake ƙarfafa miki gwuiwa ko da kin fuskanci ƙalubale?

‘Iyalan gidanmu suna taimaka min a ko da yaushe. Suna cewa aikin da nake yi abu ne mai muhimmanci. Haka ma abokanai na, su ma suna goyon bayana.

Kuma a wurin da nake aiki ma ana yaba min sosai. Idan ma an sami matsala, wannan ne abun da ke ƙarfafa min gwiwa in ci gaba da aikin da nake yi.

Mata na fuskantar ƙalubale a rayuwa, ko za ki ambato wasu daga cikinsu?

Mutane ba su cika kallon cewa mata za su iya cimma wani abu ba a fannin kimiyya. Mutum ba zai furta da bakinsa ba, amma kana iya ganewa ta yadda yake kallonki idan kuna aiki tare.

Suna kallon tun da ke mace ce kuma kin taho daga wata ƙasa ce wato Nijar, saboda haka ba za ki iya yin aikin ba. Amma ni ina yin aiki ne yadda mutane za su sauya ra’ayinsu da zarar sun ga yadda nake gudanar da aikin.

Dr Fadji Maina ta NASA

Akwai mata da burinsu shi ne su kai irin matakin da ki ke a yanzu. Me za ki faɗa musu domin ƙarfafa musu gwuiwa?

Su ba da ƙokari, su mayar da hankali. Ka da su saurari abin da mutane ke cewa a gare su.

Me za ki gaya wa iyaye kuma?

Mata suna iya yin komai kamar maza, musamman a wajen aikin kimiya. Muna buƙatar mata su shigo su bayar da nasu ƙwarewar da tunaninsu, kuma iyaye su riƙa taimaka wa ‘ya’yansu mata.

Mene ne babban burin da kike son cimma a nan gaba?

Ina so in taimakawa matan Nijar cewa su ma za su iya samun ci gaba, su yi aikin kimiyya. Idan na koma Nijar ina so in taiamaka wa matan Nijar da ke yin aiki a fannin kimiyya domin karfafa musu gwuiwa har ma da sauran matan Afirka tun da ba na Nijar ne kawai ke fuskantar ƙalubale ba.

Za ki iya koma wa Nijar nan gaba idan aka buƙaci ki yi haka?

Zan dawo. Nijar ƙasata ce domin duk in da zan tafi ina tunawa da Nijar ƙasata ce. Uwayena suna Nijar. Ina iya komawa Nijar domin bauta wa ƙasata.

Tushen Labari

Karin Wasu

Sababbin Wallafa