Connect with us

Fasaha

Ranar backup ta Duniya 31 ga watan Maris 2020

Published

on

backup day 31 tuesday 2020

Ranar backup ta Duniya a shekara ta 2020, wanda bisa al’ada wannan rana tana kasancewa ne a 31 ga watan Maris a kowacce shekara.

Wannan babban al’amari ne mai matukar muhimmanci ga duk wanda ke amfani da na’urorin zamani wajan gudanar da aiyukan yau da kullum.

Kalmar backup tana nufin sake ajiye ko adana kayayyaki a wata ma’ajiya ko ma’adana ta daban, domin magnace hadarin sulwantar su a kowanne lokaci.

Mukan dana kayan aiki (data da information), Hotuna, Bayanai cikin Sauti, Fayafayen Bidiyo, rubuce-rubuce, Litattai da sauran kayayyaki. Wanda su wadannan na’urori basu da tabbas, zasu iya samun matsala a kowanne lokaci. Wata matsalar ma takan jawo sulwantar dukkanin abubuwanda aka ajiye ko a ciki. Kacokam za’a iya sace na’urar, konewa ko faduwa ta tarwatse.

Saboda haka sake adana dukkan kayayyakin da muke da su a na’urorin mu a wata ma’ajiya ta musamman ba ma guda daya ba wurare da dama, duba da muhimmancin su a agare mu. Akwai wadnada idan suka sulwanta an rasa su kenan har abada.

Ga masu tara abubuwa a kan Wayoyi ko Kwamfutoci, lallai akwai bukatar suyi hanzarin samarwa kansu wasu ma’adanai domin gudun asara akowanne lokaci. Za a iya amfani da sabuwar hanyar zamani ta Cloud domin adana backup ko ince kayayyaki masu muhimmanci a gare su.  Za a iya snay su a fayafyan CD ko DVD, Ma’adanar kwamfuta ta waje (External Hard Disk Drive), Flash Drive mai babban rumbu, suma wadannan abubuwan sai a boye/ajiye su a wajan da baza su sami matsala ba.

Muna fatan Allah ya amfanar damu baki daya.

Continue Reading