Connect with us

Fasaha

Za a zaftare farashin data fiye da kaso 50 cikin 100

Published

on

DR. ISAH ALI PANTAMI

Za a zaftare farashin data fiye da kaso 50 cikin 100 bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bawa hukumar kula da kamfanonin sadarwa NCC na fito da matakan aiwatar da hakan a hukumance.

Ministan sadarwa  Dr. Isa Ali Pantami, ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a yau, ya ce matakin ya yi daidai da umarnin da ya bawa hukumar ta NCC na bijiro da matakan rage farashin Datar domin sauƙaƙa wa jama’a.

Dr. Pantami yace “Yanzu za a riƙa sayar da Data 1GB a kan Naira 487, a maimakon N1000 da aka saba sayarwa a baya,”

A cewarsa, ministan ya ƙaddamar da wani kwamiti da zummar samar da sauƙi wajan amfani da Data, da ake sa ran zai ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2025.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da shirin a ranar 19 ga watan Maris na shekarar nan da muke ciki ta 2020.

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku